Yadda saurayi ya siyawa budurwa sabuwar mota a ranar da suka fara haduwa

0
503

Wata budurwa mai suna Lassie, ta bayyana yadda saurayinta ya bata kyautar mota a ranar da suka fara haduwa bayan sun fara yin soyayya a waya.

Wannan dai na zuwa ne bayan wata budurwa mai suna Nara Ozim ta bayyana yadda ita ma saurayinta da ta fara haduwa da shi ya aika mata da kudi har naira dubu dari biyar (N500,000) zuwa asusun bankinta.

A cewar Lassie, ta je gidan saurayin nata a cikin motar haya, kawai sai ya yanke shawarar ba ta kyautar sabuwar mota.

Ta ce:

“Akwai wani lokaci dana taba haduwa da wani saurayi, kuma ya siya mini sabuwar mota a ranar da muka fara haduwa. Ina da kudin da zan iya siyan mota, amma bani da juriyar tuki, kuma bana son daukar direba. Haka ya sanya dole na kira motar haya, abin mamaki ina zuwa ya kira wani mai sayar da motoci ya bukaci ya aiko da sabuwar mota. Wani lokacin maza suna da yin abu cikin gaggawa.”

Post Source Twitter

Wannan dai ba shine karo na farko da samari ke siyawa ‘yammata motoci domin su burge su ba, musamman a Najeriya da ake ganin hakan wani salo ne na nuna soyayya.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here