Yadda na yaudaro kannaina guda 3 suka biyo ni harkar karuwanci – Cewar budurwa da ta kware a karuwanci

0
420

Wata budurwa mai shekaru 28 da aka bayyana sunanta da Vivian Francis, an cafke ta a jihar Edo bayan ta jawo kannanta guda uku zuwa harkar karuwancin.

Rundunar hukumar NAPTIP ta jihar Edo ce ta kama Vivian, an kama ta da yaudaro ‘yan uwan nata daga jihar Cross River zuwa Benin City domin yin karuwanci.

A wata sanarwa da kwamandar rundunar NAPTIP, Mrs Ijeoma Uduak, ta fitar, Vivian ta yaudaro kannan nata masu shekaru 15, 17, da kuma 18 zuwa Benin City, da cewar za ta sama musu aikin yi.

An kamata a wani fitaccen otel a lokacin da ake kan dokar hana zirga-zirga, inda kuma ta amsa laifinta.

Uduak ta ce an gurfanar da Vivian a gaban mai shari’a Isoken Erameh na babbar kotun jihar, inda aka yanke mata hukuncin shekara guda a gidan yari ko kuma ta biya tarar N125,000.

“Mun cafke mai laifin a lokacin dokar hana fita a wani fitaccen otel dake Benin. Ta amsa laifinta, inda ta ce taje Cross River ta kawo kannanta mata guda uku, wadanda ke da shekaru 15, 17 da kuma 18. Ta sanar da su cewa za ta taimaka musu ta sama musu aikin yi, amma a lokacin da suka iso Benin, sai ta fara amfani da su ana lalata da su tana karbe kudin.

“An kama ta da laifin karya dokar sashe na 13 na dokar NAPTIP. Kuma ta amsa laifinta, inda aka yanke mata hukuncin shekara daya a gidan yari, ko kuma tarar N125,000.” Cewar sanarwar.

Uduak ta bayyana cewa tuni an mika yaran guda uku zuwa wajen iyayensu a jihar Cross River.

Da aka tambayeta, Vivian ta ce tana dana sanin abinda tayi.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here