Yadda na sha da kyar a lokacin dana ke dauke da cutar Coronavirus – El-Rufa’i

0
167

A karon farko gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ya bayyana halin da ya shiga a lokacin da ya kamu da cutar Coronavirus.

El-Rufai wanda aka tabbatar da ya kamu da cutar a ranar 28 ga watan Maris, an killace shi na tsawon kwanaki 26 kafin ya samu sauki a sallameshi, an gwada shi sau biyu lafiyar shi lau bayan warkewa daga cutar.

A wata hira da aka yi da harshen Hausa da gidan rediyon Kaduna a jiya Talata da daddare, ya ce ya sha fama da matsanancin ciwon kai da zazzabi a satin farko da aka killace shi.

Ya kara da cewa duk da bashi da tabbacin yaushe ne ko kuma a ina ya dauko cutar, ya bayyana cewa yana da yakinin ya dauko cutar a babban birnin tarayya ne a lokacin da ya hallaci taruka da dama.

Gwamnan ya ce: “Na sha wahala sosai, an killace ni tsawon kwanaki 26 ba tare da na gana da matata ko ‘ya’yana ba, a takaice babu wanda nake gani idan ba ma’aikatan lafiya ba. Hatta mutumin da yake kawo mini abinci ya rufe dukkanin jikinshi saboda kada na goga mishi, kuma kullum ina cikin shan magani, wani lokacin sau biyu a rana.

Ya ce shi bai ji alamun tari ko sauran matsaloli na numfashi da aka ce ba, amma ya sha fama da matsanancin ciwon kai da zazzabi, wanda ya ce ko makiyanshi baya fatan suyi irin shi.

Gwamnan ya ce duk da dai babu wani daga cikin iyalinshi da ya kamu da cutar, amma yace abokin aikinshi, da daya daga cikin direbobinshi, mai aikin gidanshi, da kuma abokinshi duk sun kamu.

“Babu ko mutum daya da ya kamu da cutar a cikin iyalina, ADC dina wanda koda yaushe muke tare shi ma bai kamu ba, amma daya daga cikin direbobina ya kamu, hakan yake nuna cewa wannan cuta akwai abin mamaki a tare da ita, wadanda kake tunanin zasu kamu da ita ba sune suke kamuwa da ita ba,” ya ce.

Da yake cigaba da bayani, ya ce, “Naji mura kafin ayi mini gwaji, amma na sha wasu magunguna kuma na warke amma ciwon kai din ya cigaba da damuna. Ko lokacin dana fara jin ciwon, mataimakiyar gwamna Dr. Hadiza Balarabe ta kalle ni ta ce akwai alamun gajiya a tare dani, ina bukatar na huta. Sai ta bukaci a bani wasu magunguna, aikuwa washe gari naji sauki, sai dai kawai ciwon kan da ya cigaba da damuna.”

Ya ce kwanaki biyu na farko da aka killace shi lafiyarshi lau, amma ya bayyana cewa a kwana na ukun ne. Sai yaji wani azababben zazzabi wanda ya shafe kwanaki uku yana fama da shi, ya ce ko karatu baya iya yi, hatta salla ma sai da ta so ta gagare shi.

“Bayan mako daya sai na fara samun sauki, na fara karatu a yanar gizo akan cutar Coronavirus, sai kuma na cigaba da amfani da lokacina wajen addu’a da karatun Al-Qur’ani, daga baya kuma sai na fara halartar taron da mataimakiyar gwamna take hadawa ta yanar gizo,” ya ce.

Da yake magana akan aske kasumbar da ta fito mishi a lokacin da yake killace, gwamnan ya ce ya aske ne sanadiyyar umarnin da mahaifiyarshi ta bashi.

Ya ce duk da yaji yana son tara kasumba, amma dole ne yabi umarnin mahaifiyarshi idan har yana son ya zauna lafiya.

Gwamnan ya roki mutanen jihar Kaduna da suyi hakuri akan dokar da gwamnatinsa ta dauka akan dakile yaduwar cutar ta Coronavirus a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here