Yadda N200 ta zama sanadiyyar mayar da ‘ya’yan uwar dakina guda 2 tamkar matana – Cewar wani dan aiki

0
863

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta ce wani saurayi mai shekaru 26 da suna Chinedu Obi, ya amsa laifinsa na cewa yana kwanciya da ‘ya’yan maigidansa wadanda suke tagwayene masu shekaru 12 tun daga shekarar 2019 zuwa yanzu.

Obi wanda ‘yan sanda suka kama shi a ranar 16 ga watan Yuni, 2020, an tsare shi a ofishin ‘yan sanda na Aguda.

Matashin saurayin ya ce: “Na jima ban kwanta da mace ba, na kuma jima ina neman dama ta zo mini, ai kuwa wata rana ina shagon matar, sai daya daga cikin ‘ya’yanta ta dawo daga makaranta, sai ta shigo cikin shago ta cire kayan makarantar ta canja wasu ba tare da kunyar ina ciki ba.

“Ai kuwa ganin haka sai nace mata zan dinga bata kudi da yawa idan har za ta dinga bari ina lalata da ita.

“Nayi mamaki sosai da ta yarda ba tare da ta yi mini ihu ba. Ai kuwa a wannan lokacin na kwanta da ita na bata naira dari biyu. Nayi mamaki dana ga ‘yar uwarta ita ma ta zo tana so nayi da ita.” Cewar saurayin kamar yadda The Vanguards ta ruwaito.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sandan jihar, Bala Elkana, ya ce wata mata mai kimanin shekaru 30 ta kai kara ofishin ‘yan sanda na Aguda cewar dan tallar ta, Chinedu Obi, yana lalata da ‘ya’yanta tagwaye guda biyu.

Elkana ya ce wanda ake zargin yana hakan ne ganin cewa mahaifiyar yaran tana fita tana barin shi tare da su a gida.

“An kama mai laifin kuma ya amsa laifinsa. Kwamishinan ‘yan sanda, Hakeem Odumosu, ya umarci a kai shi bangare nau’in jinsi dake helkwatar jihar domin cigaba da bincike da kuma yanke masa hukunci,” ya ce.

Elkana kuma ya kara da cewa a wani rahoto makamancin haka, ofishin ‘yan sanda na Bariga, a ranar 26 ga watan Yuni da misalin karfe 7:50 na dare, sun karbi rahoto cewa wani dan shekara 33 mai suna Chibuike Kalu, wanda ya yiwa ‘yar shi ‘yar shekara 14 fyade.

“An kai yarinyar cibiyar lafiya ta Mirabel dake Ikeja, domin duba lafiyarta. An kuma kama Kalu, inda ya amsa laifinsa. Za a mika shi gaban kotu nan bada dadewa ba,” ya ce.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here