Wani mutumi dan kasar Afrika ta Kudu ya hau shafinsa na Twitter, inda yake bayyana labarin shi mai ban tausayi akan yadda ya rabu da matarsa da suka yi aure tsawon shekara biyu.

Mutumin mai suna @DMlamla, ya ce shi da tsohuwar matar tashi sunyi soyayya tsawon shekaru bakwai, kuma sunyi aure tsawon shekara biyu, sai ya fara ganin canji a wajenta a lokacin da ta samu aiki. Daga baya ya gano cewa tana zuwa wajen tsohon saurayinta. Kokarin da yayi wajen jawo hankalinta gare shi ya tafi a banza, saboda ta sanar da shi cewa har yanzu tana son tsohon saurayin nata, kuma shine dama wanda take so tun asali.

Ga dai abinda ya ce:

“Labarin rabuwa ta da matata. Mun yi shekara 7 muna soyayya, sannan muka yi aure na tsawon shekara biyu. Ta samu aiki, kawai sai na fara ganin canji a wajenta.

“Na kamata sama da sau uku ita da tsohon saurayinta, amma ta cigaba da cewa sun rabu, nayi kokarin daidaita abubuwa tsakanina da ita, amma abu bai yiwu ba. Na kira iyayena suma basu samu damar shawo kanta ba.

“Daga baya ta sanar dani cewa zai yi wuya ta iya rabuwa da shi saboda tana matukar son shi. Dalilinta shine tayi aure da wuri, kuma suna matukar son junansu da tsohon saurayinta hakan ya sanya baza su iya rabuwa ba.

“Hankalina ya tashi sosai, wannan shine karo na farko dana fara yiwa mace kuka a rayuwata, bazan manta yadda na durkusa ina rokonta akan ta yi hakuri ba.

‘Abinda ya sanya na yanke shawarar rabuwa da ita shine, lokacin da ta gaya mini cewa dama can tsohon saurayinta shine mijin da take mafarki, kawai ni dai ta san mutum ne mai kirki, amma zaman da take yi dani kawai zama ne take yi na hakuri.

‘Kawai dai abinda na sani shine baza ka taba yin daidai ga mutumin da ba naka ba.”

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here