Yadda mahaifina yayi mini cikin shege sannan ya tilasta ni na zubar da cikin – Cewar budurwa ‘yar shekara 19

0
606
young attractive and sad black African American woman sitting depressed at home sofa couch feeling anxious and frustrated suffering depression problem and anxiety crisis or terrible headache

Wata budurwa mai shekaru 19 a duniya, ta bayyana yadda mahaifinta mai shekaru 61 ya dinga kwanciya da ita sama da shekara daya a gidansu dake Ikorodu, cikin jihar Legas.

Wani rahoto da Vanguard ta fitar ya bayyana cewa mutumin mai suna Eke Kanu, ya kori matarsa bayan rikici ya barke tsakaninsu.

Biyu daga cikin ‘yan uwanta mace da namiji suma sun bi mahaifiyar ta su, inda suka barta ita ka dai da mahaifinsu. Yarinyar wacce take daliba ce a makarantar sakandare, ta bayyana cewa: “Mahaifina ya fara kwanciya dani shekarar da ta wuce. Duk lokacin da yayi lalata dani yana yi mini gargadin kada na gayawa kowa, inda ya ce zai yi mini duka idan na fada. A wannan lokacin da aka hana zirga-zirga na gano cewa jini na baya zuwa, sai na sanar da mahaifina. Bayan anyi gwaji a asibiti, sakamako na fitowa ya nuna cewa ina da ciki.

“Ya kai ni wani shagon sayar da magani, inda aka bani magani da allurai,” ta ce.

Vanguard ta gano cewa, mutanen yankin da suka gano cewa ya tilasta ta wajen zubar da cikin, sun sanar da kungiyar lauyoyi mata ta duniya, inda su kuma suka sanarwa ‘yan sanda.

A karshe dai an kama Kanu da kuma ma’aikaciyar lafiyar da ta bayar da maganin zubar da cikin, budurwar a cewar jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sandan jihar, DSP Elkana Bala, “an kai ta cibiyar lafiya ta Mirabel don tabbatar da lafiyar ta. Haka mahaifinta an kai shi ofishin binciken manyan laifuka dake Yaba, don yin bincike da kuma yanke masa hukunci.”

Amma ita ma’aikaciyar lafiyar, kamar yadda aka ruwaito, za ta iya neman beli a kotu.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here