Yadda kowa yabi ya tsaneni saboda na auri bakar fata – Baturiya ta bayyana labarinta mai ban tausayi

0
578

Wata Baturiya ‘yar kasar Bulgaria, ta nuna damuwarta akan wariyar launin fata, da kuma yadda ake cin zarafin mutane saboda kalar fatarsu.

Ta ce a kauyen da ta taso na Shumen, dake kasar ta Bulgaria, mutanen kauyen suna da wata matsala da babu dama su ga wani ya auri mutumin da ba kalar shi ba sai su fara maganganu marasa dadi.

Matar mai suna Elina ta ce dole ya sanya suka koma cikin birni da zama, suka fara sabuwar rayuwa, amma duk da haka rayuwar ba sauki.

Ta ce sun kasa samun gidan da za su kama haya, saboda yanayin kalar fatar mijinta, ta ce a lokacin ne ta san abinda ake kira da wariyar launin fata.

Elina ta ce ita tana daukar mutum da muhimmanci ne ta hanyar la’akari da dabi’u, soyayya, kirki da kuma mutuntaka. Ta kara da cewa tana fatan lokaci zai zo da mutane za su daina wannan bakar al’adar ta nuna wariya ga wasu mutane daban.

Wannan dai na zuwa ne yayin da ake ta faman zanga-zanga manyan kasashe na duniya akan nuna wariyar launin fata da ake yi a kasashen Turawa musamman ma ga bakar fata.

Zanga-zangar ta samo asali ne bayan kashe wani mutumi mai suna George Floyd da ‘yan sandan kasar Amurka suka yi babu gaira babu dalili, saboda kawai Allah yayi shi bakar fata.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here