Yadda iyayena suka kore ni daga gidanmu bayan na Musulunta – Maryam Abdulkareem

0
7637

Sunana Abdulkareem Ngozi Maryam, na tashi a cikin addinin kiristanci saboda iyayena duka kiristoci ne dake zama a yankin gabashin Najeriya.

Gaba daya rayuwata na dauka cewa addinin kiristanci shine addinin da yafi ina yiwa Musulunci wani irin kallo na daban. Kai har ce mana aka yi ma kada mu sake muyi abokantaka da Musulmi, saboda za su iya juya mana ra’ayi ta hanyar yadda suke tafiyar da rayuwarsu. Wannan shine fahimtar da na yiwa Musulunci har zuwa lokacin dana shiga jami’a.

A lokacin da na shiga jami’a kowanne harkoki na addini tare dani ake yi, ina ta kiran mutane akan su karbi addinin kiristanci. Ban yadda nayi abokantaka da Musulmi ba har na gama shekara ta farko a jami’a, saboda idan har bana aji to ina can tare da mutanen mu na coci.

A shekara ta biyu a lokacin da nake kan hanyar komawa makaranta, sai na hadu da wata budurwa ‘yar ajinmu Musulma sanye da Hijabi. Ita ce ma ta fara gaida ni, amma ni ban ma gane ta ba, sai daga baya ta bayyana mini ko ita wacece, ta ce mini Maryam, har ta kira sunana, a lokacin ne na gane cewa ajinmu daya. Muna da yawa a ajinmu, amma saboda na fi damuwa da harkokin addini yasa ban ma san ‘yan ajinmu ba, kadan na sani daga cikinsu sai kuma shugaban ajinmu.

Haduwa ta da wannan ‘yar ajin tamu shine farkon abinda ya fara canja akala ta zuwa Musulunci. Mun zama kawaye daga baya, kuma ta canja mini tunani baki daya akan Musulunci ta hanyar yadda take tafiyar da rayuwarta. Tana da mutunci sosai. Tana taimakawa duk wanda taga yana neman taimako.

Wata rana na tambayeta akan addininta, inda nake tambayarta ya aka yi ta zama daban da sauran Musulmai. Na tambayeta Musulmai nawa ne na hadu dasu banda ita, sai ta ce mini babu. Sai ta kai ni wajen abokananta Musulmai, sai naji sun shiga raina sosai saboda naga ainahin addinin Musulunci a tare dasu.

Na fara binsu wajen Tafsiri a lokacin azumin watan Ramadana a shekarata ta uku a jami’a, duk da dai cewa banyi azumi ba, kuma ina cigaba da zuwa coci a lokacin. Amma a wannan lokacin ne ido na ya bude akan yadda addinin Musulunci yake. A karshen zangon karatun mu na farko sai na siyo Qur’ani mai fassarar Turanci na fara karantawa. A lokacin ne na yanke shawarar zama Musulma saboda naji na kara samun kusanci da Allah ta wannan Qur’ani.

Ina komawa makaranta na gayawa kawata cewa ina son Musulunci kuma a shirye nake na koyi addinin, taji dadi sosai, amma tayi bakin ciki bayan ta tambayeni yadda iyayena za suyi idan suka ji labari. Na gaya mata cewa ba damuwa na san yadda zanyi, duk da cewa na san za suyi fushi dani sosai.

Ina komawa gida na sanar da iyayena akan sabon addinina, ai kuwa kamar na sani sai suka yi fushi dani, abinda ban taba tunani ba shine har cewa suka yi na fita na bar musu gida naje na cigaba da rayuwa da Musulmai ‘yan uwana. Duk kokarin dana yi na ganin na shawo kansu hakan bata samu ba. Sun kore ni daga gidan kuma suka yi alkawarin baza su kara nema na ba har abada, saboda na tashi daga ‘yarsu.

Naje na sanar da kawata halin da nake ciki, sai ta kai ni gidansu tace na cigaba da zama har zuwa lokacin da iyayena zasu canja ra’ayinsu su daina fushi dani, amma duk da haka iyayena sun ki saurarata.

Na rasa iyayena wadanda nake so fiye da komai, amma na godewa Allah da ya bani wani sabon dangin a cikin Musulunci. Duk da dai na san ba sauki lamarin, amma duk da haka ina godiya ga Allah ganin cewa ni Musulma ce.

A lokacin dana yi aure iyayena basu zo bikina ba, sai dana kira daya daga cikin ‘yan uwan Babana ya tsaya mini a matsayin Walih. Dana haihu mahaifiyata bata zo ba, ko murna bata yi mini ba. Ina kewar ‘yan uwana duka, amma ina fatan watarana za su gane gaskiya su dawo dani cikinsu.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here