Yadda Hassan ya yiwa Hussaini gunduwa-gunduwa da adda bayan rikici ya hado su akan budurwa

0
4657

Wani abin takaici ya faru a Ndimoko Arondizuogu, dake jihar Imo a ranar Litinin 25 ga watan Mayu, inda wani saurayi mai suna Peter Ogbonna, ya yiwa dan uwanshi wanda suke tagwaye, mai suna Paul gunduwa-gunduwa da adda bayan rikici ya hado su akan budurwa.

Rikicin ya samo asali bayan Paul ya daki dan gidan budurwar Peter, wanda yazo gidansu ya duba ko mahaifiyarsa tana nan.

A yadda rahoto ya bayyana, Paul bai goyon bayan soyayyar dake tsakaninsa da matar wacce aka bayyana cewa tana da ‘ya’ya har guda biyar.

Sai dai kuma, a lokacin da Peter yaji labarin abinda Paul yayi sai ya dauki adda mai kaifi ya tinkari dan uwan nashi. Cacar bakinsu ta juye ta koma fada, inda Peter yayi amfani da addar da ya dauka ya dinga saran Paul da ita.

Cikin gaggawa aka garzaya da Paul zuwa babban asibitin gwamnatin tarayya na Owerri, domin ceto rayuwar shi. Yayin da shi kuma Peter tuni ‘yan sanda sun cafke shi sun tafi dashi ofishinsu.

Idan ba a manta ba a jiya Press Lives ta kawo muku rahoton yadda wasu matasa suka kashe wani matashin saurayi a jihar Bauchi akan wayar salula.

An bayyana cewa saurayin yana aikin gadi a wani otel dake garin na Bauchi, sai aka nemi wayar aka rasa, su kuma masu wayar suna ganin babu wanda zai dauki wannan waya sai wannan mai gadi, hakan ya sanya suka haushi da duka da niyyar ya bayyana musu ainahin inda wayar take.

Sai dai kash; a garin haka suka yi masa dukan da har ya daina motsi, a yayin da suka nufi asibiti dashi kuwa rai yayi halinsa, inda daga baya kuma aka samu wayar a wajen wani mutumi daban.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here