Yadda dana direban jirgin sama ya kamu da cutar coronavirus – Inji Adama ta ‘Dadin Kowa’

0
5490

Fitacciyar jaruma Hajiya Zahra’u Saleh, wacce aka fi sani da Adama matar Kamaye ta cikin shirin ‘Dadin Kowa’ da ake gabatarwa a gidan talabijin na Arewa24, ta bayyana irin halin da ta shiga sanadiyyar killace danta da aka yi saboda ya kamu da cutar coronavirus.

Jarumar ta bayyana hakan ne a wata tattaunawa da tayi da Mujallar Fim. Zahra’u ta fara bayani ne da yadda cutar ta ragargaji Kannywood, ta kuma durkusar da kowa.

A cewar ta: “A gaskiya mu ‘yan fim mun samu kan mu a cikin wani yanayi dangane da zuwan wannan cuta ta COVID-19, domin kuwa duk wasu harkoki namu sai da cutar ta tsayar da su, musamman dai yadda ake gudanar da ayyukan masana’antar.

“Sai ya zamo an daina komai, sai zaman gida, duk da dai cewa al’amarin na duniya ne, amma mu ‘yan fim abin yafi yi mana illa saboda babu yadda za mu gudanar da harkokinmu ba tare da mun taru waje daya ba, to sai kuma aka ce an hana taruwa waje daya.

“Dama can kafin a fara zaman gidan harkar ta shiga wani yanayi, to da COVID-19 ta zo sai aka karasa mu gaba daya, don haka sai muka yi mutuwar tsaye.”

Adama ta cigaba da bayani akan yadda cutar ta shafe ta kai tsaye, inda ta ce: “Sai dai duk da halin da ake ciki a lokacin kawai labarin COVID-19 nake ji, to kawai sai naji ta zo mini har gida, domin kawai ina zaune a cikin gida, sai aka bugo mini waya daga Gombe, aka sanar da ni an killace dana da ya dawo daga Abuja, saboda ya kamu da cutar COVID-19.

“Nan fa na kara shiga tashin hankali, domin a lokacin sai na ji kamar ni cutar ta kama. A yadda na ji, na shiga cikin tashin hankali, domin ni a rayuwa ta ban taba ganin irin wannan yanayin ba.

“Na ce mun shiga uku! Abin da muke jin sa a nesa, yau ga shi ya zo gare mu, Allah ka kawo mana dauki.

“Wallahi na shiga tashin hankali da ban taba shiga ba, domin yaron direban jirgin sama ne, ya baro Abuja, yana zuwa Gombe sai kawai aka killace shi aka ce ya kamu da cutar.

“To kuma Allah ya kawo mana saukin abin, domin bayan kwana takwas da aka kara gwada shi sai aka ce an gano baya dauke da cutar. Tun daga wannan lokacin na fita daga tashin hankalin dana shiga.

“Wannan cuta dai ko ba ta kama ka ba, ka ji an ce wani naka ya kamu da ita, to ji zaka yi kamar ta same ka. Don haka ina rokon Allah ya kawo mana karshen wannan cutar, domin ni tun da nake ban taba shiga cikin tashin hankali kamar na wannan lokacin ba.”

A karshe Zahra’u ta yi kira ga jama’a da su dinga kiyaye kan su da kuma bin dokokin da hukumomin lafiya suka tsara domin kaucewa yaduwar cutar a cikin al’umma.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here