Yadda ake amfani da citta, lemon tsami da gishiri wajen sanya hakora suyi fari

1
7844

Hakori yana daya daga cikin muhimman abubuwa a jikin dan adam, wanda idan suka lalace kamar wani sashe na jikin mutum ya lalace ne, haka kuma duk lokacin da mutum ya fara ciwon hakori duk inda hankalinsa yayi dubu sai ya tashi, saboda wata baiwa da Allah yayi ta hada jijiyoyinsu da kusan kowacce gaba ta jikin mutum.

A lokuta da dama mutane kanyi sakaci da gyara hakoransu, wasu kuma hakan na faruwa ne saboda rashin isasshen kudi na neman abin wanke hakori mai inganci.

Wannan dalilin ne ya sanya Press Lives ta nemo muku abubuwa guda uku wadanda muke amfani da su koda yaushe kuma muke dasu a ko ina, da mutum zai yi amfani dasu wajen gyara hakorin shi yayi fari tas.

Wadannan abubuwa ba komai bane illa:

  1. Lemon Tsami
  2. Citta danya
  3. Gishiri

Bayan an samu wadanan abubuwa ga yadda za’a sarrafa su wajen hada wannan abin wanke baki:

Da farko za a bare bawon cittar, sai a yanka daidai misali a daka a turmi, a samu gishiri kadan a zuba sannan a dauki lemon tsamin a zuba ruwan a ciki a hada a juya su baki daya.

Bayan an gama hadawa sai a samu burushi na wanke baki a dinga dangwalawa ana goge baki dashi sau 1 a kowacce rana na tsawon kwanaki uku.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here