Yadda aka yiwa dalibar jami’a kisan gilla bayan anyi mata fyade ta karfin tsiya a cikin coci

0
449

Hukumar jami’ar Benin (UNIBEN), ta tabbatar da kisan wata daliba mai shekaru 22, mai suna Miss Vera Uwaila Omizuwa, wacce ake zargin anyi mata fyade ta karfin tsiya kuma an kasheta, inda har yanzu ba a san masu laifin ba.

Labarin abinda ya faru da ita dai an wallafa shi a wata sanarwa ta kungiyar dalibai ta jami’ar.

Mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Lilian Salami, tayi Allah wadai da wannan abu da aka yiwa dalibar, inda kuma ta mika sakon ta’aziyyar ta ga iyalan dalibar.

An gano cewa lamarin ya faru a cikin coci ne a Ikpoba hill, ranar Larabar da ta gabata.

Sannan an gano cewa marigayiyar ta tafi cocin ne tayi karatu a lokacin da aka yi mata wannan aika-aika.

Sai daga baya mai gadin cocin ya ga gawarta a cikin ruwa a lokacin da ya shiga cikin cocin bayan yaje ya karbo mukullin cocin daga wajen wanda yake ajiyewa kuma an sanar dashi cewa akwai wani a cikin cocin.

An bayyana cewa tuni ya garzaya ya sanar da mai ajiye mukullin da matarshi halin da ake ciki, inda suka isa wajen suka tarar da gawarta.

Wata majiya ta bayyanawa Daily Truts cewa, Vera taje wannan coci ita daya ne tana karatu, inda wadanda suka kashe ta suka shiga wajen suka yi mata duka sannan suka yia mata fyade suka kashe ta a wajen.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Edo, Chidi Nwabuzor ya tabbatar da faruwar lamarin, amma yace dole sai an jira gwajin da asibiti ya bayar shine kawai abinda zai bayyana yadda ta mutu.

“Mahaifin yarinyar, Johson Omozuwa, ya kai rahoto ofishin ‘yan sanda na Ipoba Hill, a ranar 13 ga watan Mayu, inda yace wasu da ba a san ko su waye ba sun yiwa ‘yar shi dukan tsiya a cikin coci lokacin da taje karatu.

“Yan sanda sun isa wajen da lamarin ya faru, inda daga nan suka wuce asibitin Enoma inda aka kaita domin yi mata magani a lokacin bata cikin hayyacinta.

“Daga baya an kai ta asibitin UBTH, sai dai kuma ajiya Lahadi, mahaifin yarinyar ya bayyana cewa ta rasu.

“Har yanzu muna cigaba da bincike, kuma muna jira asibitocin su fito da sakamako, daga jiki ne zamu gane yadda aka yi ta mutu. Mun ga abubuwa daban-daban ne a shafukan sadarwa kawai, amma bamu ga wata shaida ba.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here