Yadda aka sanyawa kyakkyawar budurwa guba a cikin abinci ta ci ta mutu a ranar bikin ta

0
316

Wata kyakkyawar budurwa da ta kware wajen kwalliya ta rasa ranta, bayan daya daga cikin kawayenta ta sanya mata guba a abinci a garin Jos, jihar Filato.

A yadda rahoto ya nuna budurwar mai suna Deborah Tushima, wacce ta kara shekara daya a rayuwarta, ta hada bikin murnar ranar haihuwarta a ranar Asabar 4 ga watan Yuli, inda ta gayyato ‘yan uwa da abokanan arziki don taya ta murna.

Sai dai kuma, a yayin da biki ke tafiya yadda ake so, budurwar wacce aka yiwa kyautar sabuwar waya mai kirar iPhone, ta fadi a wajen, inda cikin mintuna kalilan ta ce ga garinku nan.

Wani wanda lamarin ya faru a gaban shi ya rubuta cewa:

“An sanya mata guba a ranar bikin murnar zagayowar haihuwarta da daddare. har kyautar waya aka bata mai kirar iPhone 11. Akwai alamu daya daga cikin kawayenta ne ta sanya mata gubar.

“A yayin da take rawa kawai sai gani aka yi ta fadi tana ta amai, daga nan sai ta mutu. Abin ya faru a garin Jos, jihar Filato.”

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here