Yadda aka hada baki dani aka yi magudin kujerar gwamna – Tsohon SSG ya tona asiri bayan yayi murabus

0
401

Bayan sauka daga mukamin sakatare gwamnatin jihar Ondo, Hon. Ifedayo Sunday Abegunde ya bayyana yadda suka yi magudi a zaben gwamnan jihar da aka yi a shekarar 2016.

Abegunde ya bayyana haka a jiya ne a lokacin da yake hira a gidan rediyon Crest 87.7 FM dake Akure, babban birnin jihar.

“Akeredolu ba shine ya lashe zaben gwamna na 2016 ba, amma mun yi magudi muka dora shi a kujerar gwamnan jihar. Mune muka tsaya masa ya kai wannan matsayin, amma baza mu sake goyon bayan shi ba. Zai fadi zabe wannan karon,” ya ce.

Abegunde ya ce ya ajiye mukamin shi ne saboda ba zai iya cigaba da zama a cikin gwamnatin da kullum take kara sanya al’ummarta cikin wahalar rayuwa ba.

“Gwamnatin Akeredolu tana sanya mutanen jihar cikin mawuyacin hali, ni kuma ba zan iya cigaba da zama da wannan gwamnatin ba. Kowa na cikin mawuyacin hali. Baya biyan albashi akan lokaci. Maganar gaskiya Akeredolu bai yi abubuwan da ake tunanin zai yiwa talakawa ba, banda hanyar da yake ginawa,” ya ce.

Sakamakon wannan maganganu, Akeredolu ya sanya a kama Abegunde. Da yake magana ta bakin babban mai taimaka masa a fannin sadarwa, Mr. Ojo Oyewande, gwamnan ya ce a kama tsohon SSG din domin ya bayyana yadda aka yi magudin zaben jihar.

“Hakan na nufin ya san yadda aka yi, saboda haka sai ya sanar da mu,” ya ce.

Daily Trust ta gano cewa akwai yiwuwar wasu daga cikin makusanta na Akeredolu za su yi murabus.

Labarin murabus din mataimakan gwamnan jihar ya fara yawo a jiya ne bayan Abegunde ya sauka daga mukaminsa.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka:

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here