Yadda aka ceto yara kanana guda 72 daga wajen Malamar makaranta da take safarar yara a jihar Taraba

0
1733

Jami’an hukumar ‘yan sanda sun samu nasarar kama wata mai suna Mary Yakubu mai shekaru 40 a lokacin da take shirin safarar yara 23 zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Mary wacce take zaune a garin Maraban Baissa dake cikin karamar hukumar Donga cikin jihar Taraba, tana aikin koyarwa a makarantar firamare dake garin Bali.

An kamata bayan mutanen garin sun sanar da ‘yan sanda cewar sun gano ta da yaran kuma an tabbatar da cewa ba ‘ya’yanta bane.

An kai ta helkwatar ‘yan sanda dake Jalingo inda ta ce tana daukar yaran ne daga wajen iyayensu inda take musu karyar cewa za ta sanya su a makarantar firamare.

Da manema labarai suka tambayi Mary Yakubu, ta bayyana cewa iyayen yaran ne suka bata su ba tare da ta tilasta su ba don ta sanya su a makaranta.

Da ‘yan sanda suka tambayeta ta sanar da su cewa yanzu haka akwai wasu yaran da suke wajenta.

A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan jihar DSP David Misal, ya bayyana cewa iyayen yaran guda 23 wadanda 14 daga ciki maza ne 8 kuma mata, sun bayar da ‘ya’yan nasu domin ta samu duk wanda zai kula musu da su.

Daily Trust ta gano cewa wannan ba shine karo na farko da matar ta saba daukar yara daga garin ba, kuma tana daukarsu ba tare da sanin jami’an tsaro ko jami’an karamar hukumar ba.

Ta bayyanawa ‘yan sanda da kuma jami’an hukumar harkokin mata ta kasa cewa a kwanakin baya ma ta dauki yara goma.

Wata majiya daga cikin jami’an ma’aikatar matan da suka yi magana da matar ta sanarwa da Daily Trust cewa ta dauki wasu yaran guda goma daga wani kauye duka a cikin karamar zuwa wata makaranta a garin Maraban Baissa kafin a kama ta. Ta ce 9 daga cikin yara 10 da ta dauka duk ta dawo da su.

Kakakin rundunar ‘yan sandan DSP David Misal ya sanarwa Daily Trust cewa an mika matar zuwa gaban kotu, inda kuma daga baya aka gano cewa akwai wasu yaran a wajenta.

A cewar shi banda yara 23 da aka samu nasarar cetowa, akwai wasu yara 49 da aka samu damar ceto su daga wajenta inda suka zama 72.

Daily Trust ta bayyana cewa Mary Yakubu na shiga kauye ta dauki yaran daga wajen iyayensu da karyar cewa za ta saka su a makarantar firamare.

Kauyukan da take zuwa ta dauko yaran ko hanya babu, sannan babu makaranta, inda take kawo su garin Bali inda take zama, kafin daga nan ta kai su garin Maraban Baissa dake cikin karamar hukumar Donga.

Daily Trust ta gano cewa a Maraban Baissa ne matar take raba yaran ga mutane daban-daban inda ake mayar da su ‘yan aiki gida.

Tuni dai gwamnatin jihar ta shiga cikin lamarin, inda ta samu nasarar karbo yaran.

Wata majiya ta bayyawa wakilin Daily Trust cewa tuni gwamnan jihar Darius Ishaku ya kafa kwamiti da za ta nemo iyayen yaran da aka karbi yaran daga hannunsu.

Haka kuma gwamnan ya bayar da umarnin gina makarantu, asibitoci, kasuwanni, da kuma hanyoyi a kauyukan.

Majiyar ta ce ayyukan da gwamnan ya bayar da umarni tuni sunyi nisa, inda zuwa wata mai zuwa za’a kaddamar da ayyukan a lokacin da za a mika yaran ga iyayensu.

Haka kuma gwamnatin jihar za ta fara shirin wayar da kan jama’a a fadin jihar don ilimantar da mutanen kananan hukumomin akan su daina bayar da ‘ya’yansu ga mutanen da basu sani ba.

An gano cewa akwai lamura makamanta haka da suka dinga faruwa a jihar na safarar yara kanana da ba a bayar da rahotonsu ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here