Ya kashe matarsa sannan ya kashe kanshi bayan ya gano ‘ya’yan da ya kwashe shekaru yana wahala a kansu ba na shi bane

1
1075

Wani mutumi da aka bayyana sunanshi da Chris Ndukwe mai shekaru 39 da yake zaune a Victory Park Estate a Lekki, cikin jihar Legas, ya kashe kanshi bayan ya kashe matarshi mai suna Olamide Alli mai shekaru 25 a ranar 21 ga watan Yuni.

A cewar mazauna unguwar da yake, ma’auratan sun koma unguwar da zama makonni uku da suka wuce tare da ‘ya’yansu guda biyu. Suna da yaro mai shekara bakwai da kuma dan shekara uku.

Sai dai kuma rikicin ya samo asali ne bayan Chris ya fara zargi akan danshi na biyu, inda ya ce ba danshi bane.

Mazauna yankin sun ce basu san abubuwa da yawa game da ma’auratan ba sai ranar Asabar da daddare, kwana daya kafin kisan, inda suka gansu suna motsa jiki tare.

Mutumin ya fara zargin cewa dan ba nashi bane, bayan gwajin da suka yi a kasar Canada ya nuna cewa ba dan shi bane.

Daga baya ya fara tambayar matarsa, inda har ta kai ga ya caka mata wuka da yayi sanadiyyar mutuwar ta, shi ma kuma ya kashe kanshi.

Mutumin ya daure mata hannu tare da rufe mata baki, sai ya fara amfani da wukake yana yanka ta.

Ya makantar da ita ta hanyar caka mata wukar a ido, sannan ya cigaba da caka mata wukar a sassa na jikinta daban-daban. An gano cewa ya sha guba ne shi kuma bayan ya kammala kashe matar tasa.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here