Wuya tayi wuya: Mayakan Boko Haram sun gudu sun bar iyalansu a daji

2
354

A kokarin da suke yi na tsira da rayukansu, ‘yan kungiyar Boko Haram sun ranta cikin daji sun bar iyalansu, bayan sojoji sun kai musu mummunan hari.

A rahoton da jami’an hukumar sojin Najeriya suka bayar, sun samu nasarar kama mutum 72 daga cikin iyalan ‘yan ta’adar, inda 33 daga ciki duk mata ne 39 kuma yara kanana, da suka gudu suka barsu a kusa da karamar hukumar Ngala dake jihar Borno.

Manjo Janar John Enenche, ya bayyana cewa yanzu haka iyalan ‘yan ta’addar suna hannun dakarun sojin Najeriya.

A cewar shi, wasu ‘yan ta’addar kungiyar Boko Haram din guda 11 sun mika wuya ga rundunar hukumar soji ta ‘Operation Lafiya Dole’ dake jihar Adamawa.

Ya ce yawan samun masu mika wuya da ake yi daga ‘yan ta’addar na nuni da cewa aikin da sojojin Najeriya ke yi yana kyau. Haka kuma ya bayyana cewa akwai ‘yan ta’addar da yawa da suke so su mika wuya.

“Muna kira ga sauran mayakan da suka rage su fito su mika wuya. Haka kuma hukumar soji na kira ga iyaye, sarakunan gargajiya, shugabannin addini da sauransu da su ja kunnen ‘ya’yansu kada hudubar ‘yan kungiyar Boko Haram ta shiga kunnensu.

2 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here