Wayar salula tayi sanadiyyar kone fitacciyar ‘yar rawa Kodak kurmus yayin da ta saka caji take amfani da ita

0
185

An ruwaito cewa fitacciyar ‘yar rawa ‘yar Najeriya, Kodak, ta mutu a cikin daren jiya Laraba 29 ga watan Afrilun shekarar 2020.

A yadda rahoton ya bayyana, wayar salula ce ta kone ta a lokacin da ta saka caji a gidan daraktan da yake daukar su bidiyo a unguwar Omole dake jihar Legas.

An bayyana rasuwar ta jim kadan bayan zuwan su asibitin da aka garzaya da ita don ceto rayuwarta.

Fitaccen mawaki Olamide wanda ya nuna damuwarshi matuka akan mutuwar ta yayi mata addu’ar samun dacewa a lahira.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here