Wata sabuwa: Yahaya Bello ya tona asirin ‘yan siyasar da suke amfani da COVID-19 suna sanya al’umma cikin tashin hankali

0
398

A jiya Alhamis ne 2 ga watan Yuli, gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya zargi ‘yan siyasar Najeriya da amfani da annobar COVID-19 a matsayin hanyar wasa da rayukan al’ummar Najeriya.

Haka kuma ya kara da cewa cutar ta COVID-19 ba sabuwar cuta ba ce.

Gwamnan yayi wannan zargi ne a lokacin da yake magana da mambobin kwamitin amintattu na gidauniyar tunawa da Sir Ahmadu Bello, wadanda suka kai masa ziyara, rahoton The Nation.

Bello wanda ya ce ‘yan Najeriya suna cikin mawuyacin hali, ya dora laifin akan dokar hana zirga-zirga da aka yi, inda ya ce an san hakan zai sanya al’umma cikin wahala rayuwa.

Ya ce kamata yayi Najeriya tayi amfani da wannan lokaci na annobar ta samar da ayyukan yi kamar irinsu sarrafa takunkumin fuska da za ake fitar dashi zuwa kasashen da suke da cutar.

“Ya kamata mu dakata da wannan wasan. ‘Yan Najeriya suna cikin wani hali. Maimakon sanya dokar hana zirga-zirgar dake sanya mutane cikin halin kaka nakayi, mai yasa baza mu juya lamarin wajen samar da ayyukan yi ba; mu dinga sarrafa takunkumi na fuska da za a dinga fita dashi zuwa kasashen da suke da cutar? Ya ce.

Gwamnan wanda ya ce cutar ta COVID-19 ba sabuwar cuta ba ce, domin kuwa Najeriya tana da hanyar maganin cutar.

Ya bayyana cewa maimakon sanya mutane su cikin wani hali na tashin hankali, Najeriya ta fito da hanyar da za ta kawo karshen wannan cuta.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here