Wata sabuwa: Ya kamata a haramta bayar da sadaki ga mata a lokacin aure – Toni Tones

1
1904

FItacciyar mai amfani da shafukan sadarwa kuma fitacciyar jarumar fina-finan Nollywood, Gbemi Anthonia Adefuye, wacce aka fi sani da Toni Tones, ta ce ya kamata a cire al’adar bayar da sadaki baki daya.

A cewar jarumar, mata ba kadara bane, kuma ba wai anyi su don a siyar bane.

Ta ce: “A haramta al’adar bayar da sadaki. Mata ba kadara bane da ake sayawar.”

Banda jarumar ma dai akwai, fitacciyar mai rajin kare hakkin dan adam, Rene Ahmed, wacce ta taba yin aure sau daya, tun bayan fitowarta ta ce duk wanda zai aureta ba zai biya sadaki ba.

Rene mai shekaru 36 da ta rabu da mijin nata ta ce, idan har ta tashi sake yin aure, ita ce za ta biya kudin sadakin da mijin zai bata.

A cewarta sadaki ba wai dole bane a aure, saboda haka a haramta bayar da shi baki daya.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here