Wata sabuwa: Wike ya tona asirin abinda shugaba Buhari ke shirin yi a zaben 2023

4
18369

Fara zancen zaben shekarar 2023 a wannan shekara ta 2020, yayi kusa da yawa, cewar gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Jaridar ta ruwaito cewa gwamnan ya bayyana haka ne a hira da yayi da gidan talabijin na Arise TV, kamar yadda yayi watsi da zargin da ake yi masa na cewa yana shirin fitowa takarar shugaban kasa a shekarar 2023.

Gwamnan jihar ta Rivers dai ya bayyana cewa babban abinda ke gaban shi a yanzu shine bunkasa jihar Rivers. A cewar shi fara shirin siyasar 2023 a wannan lokacin ka iya dauke masa hankali akan ayyukan da ya dauki alkawari zai yiwa mutanen jihar Rivers.

“Daga yaya zan fara zancen fitowa takarar shugaban kasa a shekarar 2023, bayan na san cewa har yanzu ina da abubuwan da ya kamata na yiwa jiha ta, hakan zai dauke mini hankali ne,” cewar shi.

Gwamnan jihar ta Rivers ya ce siyasar 2023, matsalar jam’iyyar APC ce, saboda ita ce akan mulki, ba wai matsalar PDP ba ce.

Ya cigaba da bayani cewa tunda shugaba Buhari zai bar kujera a shekarar 2023, dole ne wasu daga cikin ‘yan jam’iyyarsa za su so su hau kujerar shi.

Gwamnan jihar ta Rivers ya kara da cewa yana da tabbacin cewa shugaba Buhari ba zai taba bari jam’iyyarsa ta sha kasa ba a 2023.

Ya ce: “Shugaban kasa zai gama mulkinsa, saboda haka wasu za su so hawa kujerar shugaban kasar. A PDP kujerar wa kuke ganin za ku hau, babu wanda zaku hau kujerar shi.

“Mun gama mulki shekarun da suka gabata, kuma har kun fara zancen shugabancin kasa.

“Idan har haka ta faru, ba zaku iya tsayawa ku samarwa da mutanenku romon dimokuradiyya ba, kuma shine abinda yake faruwa yanzu a APC.

“Kowa yana tunanin karbar mulki daga hannun shugaban kasa. Maimakon ku tsaya kuyi aiki kun koma kuna tunanin karbar mulki.

“Har yanzu baku san zuciyar ‘yan Najeriya ba. Abin duba a nan shine, a matsayinta na jam’iyya mai mulki, da kuma shugaban kasa ba zai taba bari jam’iyyar shi ta fadi ba.”

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

4 COMMENTS

  1. Muna jin dadin labaran da ku ke kawo mana a wannan kafa ta Press Lives, muna addu’ar Allah ya kara basira

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here