Wata sabuwa: Tsohon saurayin amaryar Hamid Ali ya nemi a biyashi duka kudin da ya kashe mata lokacin da suke soyayya

0
1004

A lokacin da aka kammala daurin aure tsakanin shugaban hukumar kwastam ta Najeriya Kanal Hamid Ali da amaryarsa mai suna Zainab Abdullahi Yahaya, dangin ango dana amarya kowa na cikin farin ciki akan wannan aure.

Kwatsam sai muka ci karo da wata takarda dake yawo a shafukan sadarwa, inda take nuni da yadda tsohon saurayin amaryar ta Hamid Ali, ya bukaci a biyashi sama da naira miliyan tara da ya kashe mata a lokacin da suke soyayya.

Takardar wacce aka fitar da ita a ranar 22 ga watan Mayu tana dauke da sunan kamfanin lauyoyi na Buba Partners, sun aika da takardar ga amaryar wacce gidansu ke a lamba 4 Bawo Road, Hausawa G.R.A, Kano.

Kamfanin ya rubuta takardar kamar haka:

“Mune lauyoyin Zubairu Dalhatu Malamai mai zune a lamba 224, Durumin Zungura Kano Municipal, muna amfani da umarnin shi wajen rubuta wannan takarda zuwa gare ki.

“Kamar yadda aka yi mana bayani, kuna soyayya da shi sama da shekaru uku, inda ya kashe kudi masu yawan gaske a gareki, inda ke kuka kika yi alkawarin aurenshi, duk da kin san cewa a zuciyarki yaudararshi kike yi, amma kika kyale shi ya cigaba da kashe miki kudi, bayan shi ya saka a ranshi cewa yana yiwa matar da zai aura hidima ne.

“Kamar yadda muka samu labari, mun samu labarin cewa kin yanke hukuncin aurar wani daban, yayin da shi kuma wanda ya dauke mu aiki yake taya ki murna, ya umarce mu damu nuna rashin jin dadin shi akan abinda kika yi, kwanaki kadan kafin aurenku, inda kika dinga jawo rikici tsakaninku babu gaira babu dalili, kika dinga ci masa mutunci. Saboda hakane yasa ya lissafa duka abinda ya kashe miki daga kan kudin da kika karba bashi da kuma wanda ya baki, da kudin tafiye-tafiye don ki biyashi saboda yanzu baki a cikin rayuwarshi ko kadan.

Photo Source: Facebook

“Saboda haka mun samu umarnin shi akan mu nemi jerin wadannan abubuwa daga gareki:

Photo Source: Facebook

A takaice dai Zubairu Dalhatu Malami ya bukaci Zainab ta biyashi jimillan kudi naira miliyan tara da dubu tamanin da daya (N9,81,207,45m).

Har ila yau Zubairu ya nemi ta dawo da wasu kayan sawa, kayan aikin kamfanin da kuma kwamfutocin kamfani dake hanunta da kannenta tare da maido da lambar mota mai dauke da sunan karamar hukumar Bichi dake gunta.

Photo Source: Facebook

Kamfanin Lauyoyin ya yi barazanar cewa akan cewa idan har Zainab ba ta biya wadannan kudade ta kuma dawo da wadannan kayayyaki da ya lissafo ba, to kamfanin zai dauki mataki a dokance bisa umarnin Zubairu Dalhatu Malami.

Source: @jacksonpbn Twitter Page

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here