Wata sabuwa: Sama da mutane miliyan 39 za su rasa aikin yi a Najeriya a 2020 – Osinbajo

0
450

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ce rashin aikin yi zai karu zuwa kashi 33.6, inda ake ganin kimanin mutane miliyan 39.4 za su rasa ayyukansu a karshen shekarar 2020, idan har kasar ta kasa kawo mafita akan wannan matsala da ake ciki.

Osinbajo ya bayyana haka ne a yau Alhamis a lokacin da yake gabatar da tsarin cigaban tattalin arziki ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa dake babban birnin tarayya.

Tsarin ya kunshi hanyoyi da dabarun da zasu taimaka wajen hana cutar taba fannin tattalin arziki a kasar nan.

Haka kuma shirin ya bayar da zabin manufofi da shirye-shirye da aka tsara don inganta tattalin arzikin Najeriya, sannan kuma zai taimaka wajen kirkirar ayyukan yi.

Mataimakin shugaban kasar ya kara da cewa sanadiyyar faduwar kudin man fetur a duniya, Najeriya za ta dinga fuskantar asarar naira biliyan 185 a kowanne watan duniya.

Ya ce: “Bugu da kari, dokokin da aka sanya akan jama’a don dakile yaduwar cutar COVID-19, sun yi mummunan tasiri akan gonaki, masana’antu har ma da kasuwanci, sufuri da kuma yawon shakatawa.

“Haka kuma an samu koma baya a fannin kudin shiga sanadiyyar faduwar farashin man fetur a duniya, koda farashin yana dala 30 ganga daya, kowanne wata za a dinga samun asarar kimanin naira biliyan 185.

“Rashin aikin yi zai karu zuwa kashi 33.6, ko kuma kimanin mutane miliyan 39.4 za su rasa ayyukansu zuwa karshen shekarar 2020, idan har ba a samo mafita ba akan wannan matsalar.

“Miliyoyin mutane za su fada matsanancin talauci, kafin wannan matsala ta zo karshe.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here