Wata sabuwa: Sama da kasa an nemi likitocin da suka zo daga China don taimakawa Najeriya yaki da Coronavirus an rasa

0
280
  • Jam’iyyar PDP ta bukaci gwamnatin shugaba Buhari ta bayyana inda ma’aikatan lafiyan da suka zo daga kasar China don taimakawa Najeriya yaki da Coronavirus suke
  • Jam’iyyar ta bayyana hakane bayan ministan lafiya na kasa ya bayyana cewa bashi da masaniya akan inda ‘yan kasar China din suke
  • PDP ta ce gwamnatin Najeriya na amfani da rayukan al’umma wajen cimma burinsu na siyasa

Babbar jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ta bawa gwamnatin tarayya awanni 48 ta bayyana inda ma’aikatan lafiya da suka zo daga kasar China domin taimakawa Najeriya yaki da annobar Coronavirus.

A wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar Kola Ologbondiyan ya fitar, PDP ta bayyana cewa tana da masaniya akan maganar da ministan lafiya Dr. Osagie Ehanire yayi, ta cewa bai san inda ma’aikatan lafiyan na kasar China suke ba.

Jam’iyyar ta ce maganar ministan ta sanya shakku a zuciyar al’umma, inda suke ganin jam’iyyar APC mai mulki tana boye wasu abubuwan. Inda suke ganin manyan jami’an gwamnati na wasa da rayukan al’umma a siyasance.

“Jam’iyyar APC mai mulki tana boye wani abu, jami’an gwamnati na wasa da rayukan al’umma wajen cimma burinsu na siyasa,” cewar jam’iyyar.

To dama dai kafin zuwan ma’aikatan lafiyar na kasar China daga inda cutar ta samo asali, hukumomin lafiya da manyan masana a fannin lafiya sunyi ta gargadi akan kada a bari su shigo Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here