Wata sabuwa: Nnamdi Kanu na son kashe Musulmai da Kiristoci ne ya mayar da Biafra kasar Yahudawa – Asari Dokubo

0
1678

A jiya Juma’a ne tsohon shugaban tsagerun Niger Delta, Asari Dokubo, yayi magana akan masu fafutukar kafa kasar Biafra.

Ya kira shugaban masu fafutukar kafa kasar ta Biafra, Nnamdi Kanu da ‘Wawa’.

Tsohon shugaban tsagerun na Niger Delta, yayi zargin cewa Nnamdi Kanu yana tallata rashin bin addini ne.

Ya ce mabiyan Kanu suna barazanar kashe Kiristoci da Musulmai ne a Najeriya domin su mayar da kasar ta Yahudawa.

Dokubo ya ce ba zai taba goyon bayan irin wadannan mutanen ba, inda ya bayyana cewa “dukkan mu ‘yan Biafra ne.”

Ya ce: “Wasu daga cikin ‘yan Biafra suna ganin suna da ikon kashe mutum ko su bari ya rayu, inda suke ganin za su kashe duka Kiristoci su rufe duka coci.”

Dokubo ya ce wasu mutanen sun fara “rushe duka wasu abubuwa da suke da alaka da abubuwan bautar mu, sun sanar da cewa kasarmu ta Biafra kasar Yahudawa ce.”

“Za su kashe duka Musulmai ne, ciki hadda ni mai ruwa da tsaki, za su kashe ni, za su kashe duka dangina, sannan za su kashe kowanne Musulmi.

“Kuma suna cewa na goyawa Nnamdi Kanu baya, wannan wawan ne kuke so nayi aiki tare da shi?

“Menene amfaninsa a cikin wannan gwagwarmaya ta mu? An tsare ni har sau 76, kuma har yanzu ban hakura ba, ban gudu ba, babu abinda zai saka na gudu.”

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here