Wata sabuwa: Musulmai sunyi kira da a tsige gwamnonin da suka bari aka yi sallar idi a jihohinsu

0
1041

Kungiyar dake fafutukar kare hakkin Musulmai ta Najeriya (MURIC) ta yi kira da a tsige gwamnonin da suka bari aka gudanar da sallar idi a jihohinsu duk da gargadin da gwamnatin tarayya ta yi akan hakan.

Idan ba a manta ba a makon da ya gabata ne gwamnatin tarayya tayi kira ga gwamnonin jihohi da kada su bari a gabatar da sallar idi a jihohinsu don rage yaduwar cutar coronavirus.

Sai dai kuma a ranar Lahadin nan 24 ga watan Mayu, jihohi irinsu Kano, Borno, Jigawa, Bauchi, Yobe da sauransu sun bar al’ummar su sun gudanar da sallar idi.

A wata sanarwa da kungiyar ta MURIC ta fitar dauke da sa hannun, daraktan kungiyar, Ishaq Akintola, ta yi kira da a dauki mataki na ladabtarwa akan gwamnonin.

Kungiyar Musulman ta bayar da hujjar cewa idan har Kiristoci za su bi doka a lokacin bikin Ista, mai yasa Musulmai baza su iya bin dokar ba tunda har yanzu ana fama da cutar a Najeriya.

MURIC tayi kira ga ‘yan majalisun jihohin da aka gabatar da sallar idin da su fara shirin tsige gwamnonin da suka bari hakan ta faru a jihohinsu.

“Muna matukar takaici akan matakin da wasu gwamnonin arewa da suka dauka akan al’ummarsu inda suka bar su suka halarci sallar idi, duk da umarnin ya sabawa gwamnatin tarayya, JNI da NSCIA.

“Wannan abu ne na nuna rashin kulawa ga rayukan al’umma, Abin kunya ne ace gwamnoni za su yi irin wannan abu duk kuwa da cewa hakan ya shafi rayuwar al’umma. Wannan ba Musulunci bane.

“Dole akwai hukunci akan mutanen da suke da mukami suka yi wasa da rayukan al’ummarsu. Wannan mataki da suka dauka ya jefa rayukan al’ummar kasar nan cikin hadari, saboda haka mu jira nan da mako biyu lokacin da kwayar cutar za ta yi tasiri a jikin mutane a lokacin zamu gane irin barnar da gwamnonin suka yi. Haka ba shine yadda ake bautar Allah ba.

“Dole ne kowanne Musulmin Najeriya dauki alhakin hakan. Abinda wadannan gwamnonin suka yi abin kunya ne ga addinin Musulunci. Dole ne mu yarda da kuskurenmu saboda abin da muka yi ka iya kawo babbar matsala ga kasa baki daya. Mako biyu masu zuwa za su bayyana komai. Amma kafin wannan lokacin, dole ne mu bawa ‘yan Najeriya hakuri akan jefa kasar cikin hadari da muka yi.

“Saboda haka kungiyar MURIC dole ta bada hakuri ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, gwamnatin tarayya da duk wani mai bin doka da oda a kasar nan. Idan har muka samu wasu wadanda suke cin zarafin Musulmai bama yin shiru, saboda haka ba zai yiwu lokacin da Musulmai suka yi ba daidai ba muyi shiru.

“Kada shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi shiru akan wannan lamari dole a dauki mataki akan gwamnonin. Dole ne a sanya musu takunkumi. Dole gwamnatin tarayya tayi magana. Saboda haka dole ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsara hukuncin da ya dace wanda zai shafi iya ofishin wadannan gwamnoni ba al’umma ba.

“Bamu ga karshen wannan annoba ba, saboda haka idan muna da ‘yan majalisar jihohi masu kishi sun san hukuncin da ya kamata su dauka akan wadannan gwamnoni.

“Maganar gaskiya hukuncin laifin gwamnonin nan tsigewa ce. Saboda haka muna kira ga ‘yan majalisar wadannan jihohi da su yi abinda ya kamata akan wadannan gwamnoni. Bamu son gwamnonin da basu son al’ummarsu. Zabi biyu ne a wajen gwamnonin: ku fito fili ku bayar da hakuri ko kuma ku tattare komatsanku ku bar gidan gwamnati, idan ba haka ba ku sani za a tsige ku.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here