Wata sabuwa: Ministan Shari’a ya bukaci Buhari ya tsige Ibrahim Magu

0
430

Ministan shari’a kuma alkalin alkalan Najeriya, Abubakar Malami, an ruwaito cewa ya rubutawa shugaban kasa Muhammadu Buhari wasika, inda ya bukaci shugaban kasar ya kwace kujerar shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa na kasa, Ibrahim Magu.

Thisday ta ruwaito cewa, a wasikar da Malami ya rubutaw shugaban kasar, ya bawa Buhari shawara ne akan dalilai da yawa da suka hada da: “karkatar da kudaden da aka kwace zuwa wata hanya da ba a san da ita ba.” Wasu majiyoyi da yawa sun bayyanawa Thisday cewa Malami ya rubuta sunayen mutane uku da yake so a maye gurbin Magu da su.

Haka rahoton ya bayyana cewa Magu shima bai zama kurum ba, domin kuwa magoya bayansa dake fadar shugaban kasa sun bayyana cewa cire Magu daga kujerar a wannan lokacin da yayi aiki tukuru wajen yaki da cin hanci a Najeriya ba karamin kuskure bane.

“Babu dadi ko kadan ace shugaban hukumar EFCC yana samun irin wannan tsaiko da har wasu suna tunanin cire shi daga mukamin shi bayan nasarorin da ya samu,” cewar majiyar.

Majiyoyin sun ce bisa la’akari da zargin da ake yiwa Magu, shugaban kasar na iya sanya kwamitin bincike wadanda za su binciko gaskiyar zargin da ake yi masa tare da bayar da shawarwarin da suka dace.

Malami yayi ikirarin cewa akasarin kadarorin da hukumar EFCC ta kwace Magu ya sayar da su ba tare da sanin kowa ba.

Haka wani mai goyon bayan EFCC ya ce:

“Malami ya kuma zargi Magu da nuna girman kai da nuna alfahari, sannan kuma yaki amincewa da shi a matsayin mai sa ido akan hukumar ta EFCC.

Idan za a iya tunawa, an yi ta kokari a shekarun baya don ganin shugaban kasa ya sauke Magu daga kujerar shi, tun bayan nada shi da yayi a matsayin mukadashin hukumar a ranar 9 ga watan Nuwambar shekarar 2015.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here