Wata sabuwa: Kowa sai yayi rijista a Masallaci kafin a bari yayi sallah – Gwamnatin tarayya

0
2821

Za a dinga yin rijista a Masallatai da coci, don bin diddigin masu zuwa bauta, a bisa ka’idojin da gwamnatin tarayya ta fitar ga cibiyoyin addini da za su bude wuraren ibada a Najeriya.

Babban jami’in kwamitin gudanarwa na cutar COVID-19, Dr. Sani Aliyu shine ya bayyana haka a jiya Talata a Abuja.

Ya kuma yi gargadin cewa duk da cewa gwamnati ta cire dokar bude wuraren ibada, amma abinda yafi shine mutane suyi ibadarsu a gida.

Idan ba a manta ba a ranar Litinin din nan da ta gabata, shugaban kwamitin gudanarwa na cutar ta COVID-19, kuma babban sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da a bude wuraren ibada amma bisa wasu sharuda.

PTF Dr Sani Aliyu Photo Source: Daily Trust

Da yake bayyana dokokin a jiya Talata a wajen taron da kwamitin ta saba gabatarwa kowacce rana a Abuja, Aliyu ya ce daya daga cikin dokokin sune dole kowanne Masallaci da Coci sai sun bude rijista da za ta taimaka wajen bin diddigin masu zuwa ibada.

KU KARANTA: A karshe dai gwamnati ta cire dokar hana zuwa Masallaci da coci a fadin Najeriya

A cewar shi saboda yanayin wuraren ibadar mu, cutar ta coronavirus ka iya yaduwa cikin gaggawa tsakanin al’umma.

“Gwamnatin tarayya ta yanke shawarar sake bude wuraren bauta a bisa wasu ka’idoji na musamman, amman idan mutum zai iya yin ibada a gida hakan zai fi, domin yin ta a gida yafi fiye da fita wajen bautar a wannan lokacin.

“Saboda gujewa yaduwar cutar, yana da matukar muhimmanci wuraren bautar suyi aiki cikin amince don tabbatar da lafiyar al’umma, kuma a gujewa barkewar cutar a cikin jama’a.

“Saboda haka gwamnati ta tsara wadannan dokoki a wuraren bauta, dokokin kwamitin PTF ce ta sanya su tare da hadin guiwar shugabannin addini na Najeriya, da su za ayi amfani a kowacce jiha don cigaba da yin bauta,” cewar Aliyu.

Ya ce yana da muhimmanci mutane su gane cewa wuraren bauta sune suke da babbar damar da yaduwar cutar za ta yi sauki a cikin al’umma.

Ya ce; “Saboda haka duk wuraren bautar da ba su iya bin wadannan matakai ba ya kamata gwamnatocin jihohi su rufe su.”

Ya kara da cewa: “Bayan ibada kuma babu wani taro da aka amince mutane suyi, sannan kuma ana shawartar tsaftace wuraren bautar a kullum; wuraren bautar za su ajiye bayanan duka masu zuwa wajen gami da adireshin da za a tuntube su.

“Saboda haka wuraren bautar da ba za su iya bin waɗannan matakan ba ya kamata gwamnatocin jihohi su rufe su.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here