Wata sabuwa: Kotu za ta binciki Sanusi Lamido kan zargin sama da fadi da N2.2b

0
510

Watanni uku bayan tsige shi daga kujerar sarautar jihar Kano, wata babbar kotun tarayya dake zama a Kano ta bayar da umarni ga hukumar yaki da cin hanci ta jihar Kano da ta fara bincike tsohon Sarkin Kanon Malam Muhammadu Sanusi II akan zargin sama da fadi da naira biliyan 2.2 na kudin filaye.

A watan Maris ne Daily Trust ta ruwaito cewar tsohon Sarkin yana fuskantar bincike daga wajen hukumar yaki da cin hancin ta jihar akan zargin sayar da wasu filaye mallakin masarautar jihar.

Hukumar yaki da cin hancin tana zargin tsohon gwamnan kudin na Najeriya da bayar da umarnin sayar da filaye mallakin Darmanawa, Hotoro da kuma Bubbugaje.

Tsohon Sarkin ya fuskanci kotun a wancan lokacin inda kotun ta dakatar da hukumar daga binciken shi akan wannan lamari.

Sai dai kuma, Mai Shari’a Lewis Allagoa, a ranar Talatar nan ta cire wannan kariya da kotun ta bawa tsohon Sarkin, inda ta ce hukumar yaki da cin hancin tana da ikon bincikar shi akan wanna lamari.

A cewar hukumar yaki da cin hancin ta jihar, tsohon Sarkin ya sayar da fili mai lamba CON-RES-2016-503 ta hanyar da bata kamata ba, ta kara da cewa an gabatar da cinikin ta hannun Shehu Dankadai (Sarkin Shanu), Sarki Ibrahim (Makanan Kano) da kuma Mustapha Yahaya (Dan Isan Lapai).

A lokacin da yake mulki dai Sanusi basa ga maciji da gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje.

A shekarar 2017, masarautar ta Sanusi an fara gabatar da bincike a kanta akan cin hanci, amma daga baya aka dakatar da binciken bayan wasu manya a Najeriya sun sanya baki a cikin lamarin.

A shekarar 2019, Ganduje ya sanya hannu a dokar kirkirar sababbin masarautu na yanka guda hudu a jihar.

A lokacin Sanusi na mulkar kananan hukumomi guda 10 ne kawai daga cikin kananan hukumomi 44 na jihar.

A watan Maris kuma aka fara gabatar da bincike akan Sanusi saboda ya karya dokar gargajiya ta masarautar jihar.

A ranar 9 ga watan Maris ne kuma gwamnan jihar ya tunbuke Sarkin daga kan kujerarshi, inda aka tura shi jihar Nasarawa, kan zargin nuna rashin da’a daga manyan jihar da kuma kin bin umarnin gwamnatin jihar na zuwa taro da ta gabatar.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here