Wata sabuwa: Kotu a kasar Indiya ta hana kiran Sallah a Masallaci, saboda mutane na fita salla a jam’i

0
173
  • Wata kotu a kasar Indiya ta sanya dokar hana kiran sallah da abin karin sautin murya
  • Kotun ta yanke wannan hukunci ne inda ta ce ta san kiran sallah na da matukar muhimmanci ga Musulmai, amma kiran sallah da lasifika ba dole bane a Musulunci
  • Musulmai dai na cikin wani hali a kasar Indiya fiye da shekaru 5 kenan tunda masu addinin Hindu suka sako su a gaba

Kwanan nan, wata babbar kotu a kasar Indiya dake Allahabad ta yanke hukuncin hana kiran sallah da lasifika a Masallaci.

Kotun ta ce: “Muna da masaniya cewa kiran Sallah yana daya daga cikin abubuwa masu muhimmanci a Musulunci, amma amfani da lasifika ko wani abin sauti ba dole bane a Musulunci, inda muke ganin hakan a matsayin hanya ta takura al’umma.

Wannan dai ya zo ne bayan wani babba a garin Ghazipur ya sanya dokar hana kiran sallah a Masallaci, inda yace hakan yana sawa mutane suna fitowa Sallah a jam’i a wannan lokaci da aka hana saboda Coronavirus.

Gwamnatin jihar dai ba ta bayyana hana kiran sallar ba, amma shugabannin garin sun yanke wannan hukunci a karan kansu.

Kotun dai ta bayyana cewa daga yanzu babu wanda zai sake kiran sallah da abin karin sautin murya ba tare da umarnin mahukunta na garin ba, idan kuma mutum yana da ja zai iya kai kara gaba akan wannan doka.

Sama da shekaru biyar kenan Musulmai a kasar India suke cikin mawuyacin hali akan sanyo su a gaba da shugabannin kasar masu bin addinin Hindu suka yi.

A yanzu haka a kasar ta Indiya mutane na yiwa Musulmai kallon sune suke sanya musu cutar Coronavirus, inda a wasu wurare da yawa ake dukan su har da kisa kan suna bautar Allah.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here