Wata sabuwa: Kasar Libya ta ce a shirye take ta gwabza yaki da kasar Masar

0
292

Ministan harkokin cikin gida na kasar Libya Fathi Basaga, ya sanar da cewa kasar ta Libya ba ta kaunar wani abu na cutarwa ya samu kasar Masar, amma idan har yiwuwar hakan ta taso to fa a shirye take da ta gwabza yaki don kare kanta.

A baya dai shugaban kasar Masar Abdulfatah Al-Sisi yayi barazanar amfani da soji a kasar ta Libya, hakan ya sanya ministan harkokin cikin gidan fito ya bayyana nasa sakon a shafin Twitter, inda yake cewa: ‘Shugabannin takwararmu kasar Masar sun manta kwata-kwata da cewa kasashen mu guda biyu suna da dumbin tarihi a baya na kaddara da kuma al’adu iri daya.”

Ministan ya ce: “Libya ba za ta yadda da duk wani abu da zai cutar da zaman lafiya a kasar Masar ba, saboda idan haka ta faru ba wai iya ita daya ce za ta cutu ba, hatta kasar Libya sai abin ya shafe ta

“Da jinin al’ummar Libya aka rubuta jan layi, saboda haka al’ummar kasar Libya za su zauna lafiya lau da duk wadanda suke da burin hakan. Haka kuma al’ummar Libya za su afka yaki ba wai domin su kai hari ba, sai don su kare kansu da kasarsu.

A daya bangaren kuma, Firaministan kasar ta Libya Fayyaz Sarraj yayi wata ganawa da kwamandan sojin kasar na kai farmaki Janar Ibrahim Ahmed Baytulmal, inda suka yi magana akan yadda za su kare al’ummar kasar fararen hula a yayin kai farmakin.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here