Wata sabuwa: El-Rufai ya tona asirin abinda gwamnoni suke yi game da cutar COVID-19

0
16790

Gwamnan jihar Kaduna Nasir Ahmed El-Rufai yayi magana akan zargin da wasu suke yiwa gwamnonin jihohi na cewa suna rage yawan mutanen da suke aikawa hukumar NCDC.

A na shi martanin gwamnan ya ce: “Kuma gaskiya ne.”

Gwamnan dai yayi raddi ne akan rubutun da wani mai suna Jibrin Ibrahim ya wallafa, wanda ya dinga bin diddigin yawan mutanen da hukumar NCDC take saki a kowacce rana.

Ibrahim ya zargi cewa gwamnonin jihohi basa aikawa da hukumar NCDC duka yawan mutanen da suka dauka, suna rage yawan mutanen don komai ya dawo daidai a jihohinsu.

“Akwai abin dubawa a yawan mutanen da NCDC take saki kowanne maraice, menene ma’anarsu? Ana aikawa da samfurin da aka gwada ta hanyar kwamitin gudanarwa dake kowanne jihohi. Wuraren gwajin suna gwada iya abinda aka ba su ne kawai. Saboda haka wanda bayar da samfurin zai iya sai ta lambar da yake so, gwamnoni suna rage yawan mutane,” kamar yadda ya rubuta a shafinsa na Twitter.

A lokacin da yake mayar da martanin, gwamnan jihar ta Kaduna ya ce ba kowacce jiha ce ke aikawa da lambobi na bogi ba. A cewar shi jihohin Kaduna, Legas da Abuja suna bayyana ainahin abinda aka samu kuma suna iya bakin kokarinsu wajen kawo karshen cutar.

Ya ce: “Zai iya zama gaskiya, amma ba duka jihohi ne suke aikawa da lambobin bogi ba, Abuja, Kaduna da Legas suna iya bakin kokarinsu wajen bin diddigin masu cutar, saboda muna son mu san ainahin masu cutar domin muyi musu magani. Muna so mu ceto rayukan al’umma ne.”

Haka ita ma wata mai amfani da shafin na Twitter, ta bayyana cewa yawan mutanen da ake aikowa daga jihohin Kudu maso Yammacin kasar akwai alamar tambaya a kansu. Ta ce ita ma kawai ta yadda da na Kaduna, Legas da Abuja ne kawai.

To sai dai wasu ‘yan Najeriyan basu ji dadin wannan martani da gwamnan yayi ba, wasu na ganin cewa siyasa ce kawai yake yi.

Wani kuwa cewa yayi yawan mutanen da ‘yan bindiga suka kashe a Najeriya yafi wadanda coronavirus ta kashe.

Ya zuwa yanzu dai jihar Kaduna ita ce ta shida a cikin jerin jihohin da suka fi masu cutar a Najeriya, inda take da yawan mutane 335.

Kuma ita ce daya daga cikin jihohin da har yanzu ba ta cire dokar bude wuraren ibada ba.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here