Wasu gwamnonin na amfani da annobar Coronavirus ne suna kwashe kudin al’umma kawai – Farfesa Ango Abdullahi

0
468

Kungiyar dattawan Arewa ta zargi gwamnatocin wasu jihohi na kasar nan da siyasantar da annobar Coronavirus domin su dinga samun kudi daga wajen gwamnatin tarayya.

Ya zuwa yanzu dai jihohi 33 da babban birnin tarayya Abuja ne annobar ta shiga. Iya jihar Cross Rivers da Kogi ne kawai cutar ba ta bulla ba.

A wata sanarwa da shugaban kungiyar Farfesa Ango Abdullahi ya fitar, ya ce abinda ya kamata gwamnati tayi a wannan lokaci shine ta zo hanyar da za ta taimaka wajen kare rayukan al’umma.

“Kungiyar bata ji dadin yadda gwamnatocin wasu jihohi na kasarnan suke amfani da halin da ake ciki domin samun kudi daga wajen gwamnatin tarayya da kuma kasashen waje.

“Kowa ya sani abinda kasar nan ke bukata a wannan lokaci shine, hanyar da za ta taimaka wajen kare rayukan al’umma ta hanyar samar da kayan aiki da magunguna kayan abinci da za a dinga taimakawa mutane da su a wannan lokaci da aka hana zirga-zirga.

“Haka kuma duk wasu ka’idoji da aka sanya a wasu bangarori na kasar nan da basu kamata ba kamata yayi a hana su.

“Bayan haka muna bukatar ayi duba wajen aikawa da kwararrun ma’aikatan lafiya zuwa jihohi, sannan ayi duba akan dalilin da yasa ake samun yawan mace-mace a jihar Kano.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here