Wale Olagunju: Faston da ya shafe shekara 20 bai yi wanka ba sannan bai yi jima’i da matarsa ba saboda wahayi da aka yi masa

0
2701

Babban faston cocin Divine Seed of God Chapel Ministries dake Ibadan, Oyo State, Wale Olagunju, ya bayyana cewa ya shafe shekara 20 bai yi wanka ba, sannan bai yi jima’i da matarsa.

A cewarsa, cocin tana kara karfi ne kuma duka wahayin da ake masa suna da nasaba da wannan abu da yake yi.

Faston ya bayyana haka ne a wata hirar bidiyo da aka yi da shi a shafin Instagram, inda ya bayyana yadda yake rayuwa ba tare da jima’i da wanka ba.

Da aka tambaye yadda yake rayuwa a haka, sai ya ce:

“Wannan umarni ne daga Ubangiji. Umarni ne daga ubangiji mai girma, kuma na gode masa, domin kuwa kuna ganin jikina bana wani. Komai lafiya lau, wani ma ba zai yarda ba.

“Ban yi wanka ba na tsawon shekara 20 cif, kuma zan iya tabbatarwa da mutane cewa wahayi ne aka yi mini.

“Na ware kai na, ina ganawa ta musamman da ubangiji.

“Ina shiga cikin daji cikin duwatsu, yawancin rayuwa ta ina yin ta a cikin duwatsu ne, kuma ina jin dadin yadda nake magana da ubangiji a kowanne lokaci.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here