Wa’iyazubillah: Za ayi bikin tukin keke tsirara haihuwar uwa a kasashen duniya duk da annobar Coronavirus da ake fama da ita

0
494

Masu hada bikin tukin keke na duniya tsirara, wanda aka saba gabatarwa duk shekara a cikin biranen duniya, sun bayyana cewa wannan shekarar ma za a gabatar da wannan biki duk da annobar Coronavirus da ake fama da ita.

Sun ce tunda wannan shekarar an samu matsalar annobar Coronavirus, za a dan samu ‘yan canje-canje a wannan karon.

A cewar masu hada wannan biki, maimakon wannan karon a hadu a wuri daya a lokaci daya, zai kasance duk wanda yake son yayi zai yi tsirara ya hau keke ya zagaya duk inda yake so a kowanne lokaci.

Birane da dama sun hana gabatar da wannan biki a wannan shekarar ciki hadda birnin Landan, St Loius, da San Francisco, amma birnin Portland, da Oregon sun ce a wannan shekarar ma zasu gabatar da bikin.

“Dole muyi la’akari da lafiyar al’umma,” cewar masu hada bikin a shafinsu na Facebook. “Mun fi cutar nan tasiri, saboda haka koda zai kasance zamu yi tsirara a cikin dakunan mu mu tuka keke ne sai munyi.”

A shekarar da ta gabata dai, sama da mutane 10,000 ne suka halarci wannan biki, inda kowa yayi tsirara akan keke.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here