Wa’iyazubillah: An kama ‘yan luwadi guda 60 a kasar Saudiyya

1
5130

A ‘yan watannin nan babbar kotun manyan laifuka ta birnin Jeddah ta yankewa kimanin mutane 60 hukunci bayan kama su da laifin aikata luwadi. Jaridar Al-Watan Daily ita ce ta ruwaito wannan rahoto.

Duka mutanen da aka kama da wannan laifi an yanke musu hukuncin bulala da kuma zaman gidan yari, babu wanda aka yankewa hukuncin kisa a cikinsu.

Haka kuma a wani rahoto makamancin haka, hukumar HAIA ta kasar ta kama wasu matasa guda biyar da suke zaune a wani wajen sayar da abinci.

An sanar da hukumar ta HAIA cewa an gano wasu mata guda uku suna zaune tare da wasu maza matasa guda biyu. Duka matan guda uku basu sanya Abaya ba, kuma duka sun sha kwalliya, cewar majiyar.

Sufeto na hukumar ta HAIA, wanda ya isa wajen sayar da abincin domin ya kama matan, ya gano cewa matan guda uku duka mata ne suka yi shiga ta maza suka sha kwalliya.

Sun bula kunnensu, sannan sun aske gashin kafarsu, ‘yan daudun sunyi kokarin guduwa, amma aka cafko su. Sufeton ya ce duka mazan guda uku sun aske kafafunsu, hannunsu da kuma fuskokinsu.

Photo Source: Life In Saudi Arabia

An yankewa wadannan ‘yan daudu hukuncin watanni hudu a gidan yari tare da bulala dari dari, inda sauran mutane biyu kuma aka cigaba da tsare su. A cewar Nasr Al-Yamani, tsohon alkali, ya ce irin wannan lamari babu wani hukunci da aka tanada akan shi, kawai dai ya rage ga alkalin kotun ya yanke hukuncin da yaga ya dace.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here