Wa’iyazubillah: An kama wani saurayi yana jima’i da alade a Najeriya

0
445

A jiya 23 ga watan Yuni ne aka gurfanar da wani saurayi mai shekaru 22, mai suna Ayokunbi Olaniyi, a gaban kotun majistire da laifin yin jima’i da alade.

Dan sanda mai gurfanar da mai kara, Insp. Opeyemi Olagunju, ya sanar da kotu cewa Olaniyi, wanda yake zaune a Eleti-Odo, a garin Ibadan dake jihar Oyo, an kama shi yana jima’i da alade a ranar 2 ga watan Afrilu da misalin karfe 4 na yamma.

A cewar Olagunju, mutumin yana aiki a wata gona ne da ake kiwon aladu a Elewi-Odo, inda aka kama shi yana lalata da daya daga cikin aladun. Ya ce an gurfanar da mai laifin a gaban kotu kan wannan laifi, wanda ya sabawa sashe 214 na dokar sharia ta jihar Oyo ta shekarar 2000.

Da aka kira shi a gaban kotun, Ayokunbi ya amsa laifinsa. Lauyan da yake kare shi Mr Mumin Jimoh ya roki kotu ta bayar da belin shi, a cewarsa mai gonar aladun tuni ya yafewa mai laifin wannan abu da yayi.

Alkalin kotun majistiren, Olaide Amzat, bayan gama sauraron korafin, ya ce:

“Idan mai aladen ya yafewa mai laifin, hakan na nufin Allah ya yafe masa? Dole sai doka tayi aiki a kanshi.”

Ya bukaci a bayar da naira dubu dari a matsayin kudin beli, tare da shaidu guda biyu.

Daga nan ya daga sauraron karar zuwa ranar 21 ga watan Yuli.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here