Umar Yusuf: Matashi dan Arewa mai fasaha da yake kera kekuna don taimakon matasa

0
511

Wani matashin saurayi mai suna Umar Yusuf, ya nunawa duniya cewa mutanen Arewa su ma ba a bar su a baya ba, bayan ya kirkiri wata sabuwar fasahar shi.

Saurayin yayi amfani da hannunshi, duk da bai samu kayan aikin da ya kamata ba wadanda za su sanya aikinshi yayi sauki, Yusuf dai yana kera kekuna ne, kekuna irin wadanda za su kawo kishi ga manyan kamfuna na keke dake duniya.

Yana aikin shi a garin Maiduguri dake jihar Borno, jihar da tafi ko ina matsalar tsaro a Najeriya.

Press Lives ta gano cewa matashin saurayin yana iya bakin kokarinshi don kera kekuna masu yawan gaske don kara karfafa guiwar matasan Najeriya.

A young man, Umar Yusuf in Maiduguri that constructed several sport bikes says he is ready to empower hundreds of young people if he has enough resources.

Posted by Northeast Reporters on Monday, July 6, 2020

‘Yan Najeriya da yawa sun yi ta yabawa Yusuf, haka kuma sun bukaci gwamnatin tarayya da ta jiha da su tallafa masa, musamman ma yanzu da Najeriya take son mutane su fi karfi wajen kimiyya da fasaha.

Misali wani mai suna Kabir Ajibola, wanda yayi sharhi, ya roki a tallafawa Yusuf, inda ya ce yana neman tallafin cikin gaggawa.

“Na tabbata gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, zai yi wani abu akan wannan, idan ba haka ba, mu muna bukatar shi a jihar Legas, gwamnan mu (Babajide Sanwo-Olu), zai taimaka masa,” ya ce.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka:

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here