Tunda ta daina bari na nayi jima’i da ita, hankalina baya tare dani – Cewar magidanci da ya nemi a raba aurensu

0
364

Wani magidanci mai suna Abidemi Dada, ya roki wata kotu dake Mapo, jihar Oyo da ta raba aurensu da suka shafe shekara 13, saboda ba ta barin shi ya kwanta da ita.

Dada, wanda yake injiniya ne dake zaune a Oke-Bola cikin garin Ibadan, matata ta canja baki daya, “rayuwata ta canja baki daya tun lokacin da matata ta fara hanani kwanciya da ita.”

“Haka kuma matar tawa tayi watsi da shawarar da Fasto din mu ya bata. Babu kwanciyar hankali ko kadan a auren mu. Haka kuma ga zagina da take yi duk lokacin da ta ga dama,” ya ce.

Alkalin kotun, Cif Ademola Odunade, ya bukaci ‘yan uwan ma’auratan da su zaunar dasu su basu shawara.

Alkalin ya ce ya gano cewa har yanzu akwai alamu na soyayya tsakanin ma’auratan, inda ya roke su da su yi hakuri.

Ya daga sauraron karar zuwa ranar 6 ga watan Agustan wannan shekara ta 2020. Rahoton (NAN).

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here