Tunda aka yi mini fyade na tsani jima’i kuma nayi sallama da shi – ‘Yar wasan Tebur Tanis

3
3081

Fitacciyar ‘yar wasan Tebur Tanis ta Najeriya. Funke Oshonaike, ta ce ta fara tsanar jima’i ne tun lokacin da aka yi mata fyade tana yarinyar.

Fitacciyar ‘yar wasan ta bayyana hakane a lokacin da take tofa albarkacin bakinta akan fyade da kuma kisan Uwa Omozuwa, budurwa ‘yar shekara 22 da aka yiwa fyade a cikin coci a jihar Edo.

“Wannan labarin gaskiya ne a kaina, babu dadin ji ko kadan, kuma ya shafi rayuwar jima’i na. Na tsani jima’i, ba zan iya bayyana baki daya labari na ba a yanzu, saboda cikakken labarina yana nan fitowa nan bada dadewa ba,” cewar oshonaike.

Haka kuma ta roki iyaye da su dinga kokari wajen bawa ‘ya’yansu maza tarbiyya ta gari, inda ta ce hakan zai taimaka wajen rage yawaitar fyaden.

“Ya taba faruwa dani, kuma na san yadda ake ji. Mata su tashi tsaye suyi yaki da wannan abu,” cewar ‘yar wasan.

“Anyi lalata dani bayan duka dana sha, yana tilasta ni wajen kwanciya dani. Sai bayan na girma ne na gane cewa ashe wannan abu da ya dinga yi mini shi ake kira da fyade.”

Oshonaike ta kara da cewa, “ya kamata iyaye su bawa ‘ya’yansu maza tarbiyya su kuma nuna musu muhimmancin girmama mata, sannan su nuna musu cewa ba a tilasta mace tayi zina da mutum, ko da kuwa da aure a tsakaninsu.”

Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne dai aka yiwa dalibar ‘yar aji daya a jami’a fyade a garin Benin City babban birnin jihar Edo, a lokacin da taje cikin coci za ta yi karatu.

Bayan yi mata fyaden an kashe ta a take a wajen, inda aka dinga neman wadanda suka yi wannan aika-aika aka rasa, sai dai an bayyana kama wasu da ake zargin suna da hannu a wannan lamari.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

3 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here