Tun muna yara muke son Buhari gashi yanzu tsufa ya kama mu bai mana uban komai ba – Hajiya ta koka

0
1775

A yayin da mutanen Arewa suke kokawa akan salon mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari, musamman a wannan lokaci da tsaro ya gama tabarbarewa a kasar.

Mutane da dama na hawan shafukan sadarwa suna bayyana ra’ayoyinsu da jan hankali ga shugaban kasar da ya dauki mataki akan kisan kiyashin da ake yiwa al’ummar yankin Arewa babu gaira babu dalili.

A na ta korafin da tayi, wata Hajiya da aka nuno a wani sabon bidiyo ta koka sosai akan salon mulkin shugaban kasar, inda ta ce abin da ake yiwa mutanen arewa yayi yawa.

Ta ce ‘yan arewa sune suka tsaya suka zabi Buhari ba tare da an basu kudi ko wani abu ba, tsananin soyayya ta saka suka jure dukan rana da yunwa suka fita suka tsaya tsayin daka suka zabi shugaban kasar, amma yanzu babu abinda ya saka musu dashi sai tsabar bakin ciki.

Hajiyar ta kara da cewa tun suna yara suke son shugaba Buhari, amma yanzu gashi tsufa yana neman riskarsu ba tare da ya tsinana uban komai a Arewa ba.

Ta ce su baza su zagi shugaban kasar ko kuma suyi wata magana marar dadi a kanshi ba, amma ya kamata dai shugaban kasar ya duba yayi adalci akan mulkin da yake gabatarwa.

Ga dai bidiyon Hajiyar da yadda take kokawa akan mulkin Buharin:

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here