Tun ina ‘yar shekara 11 kanin mahaifina yake lalata dani – Mawakiya ta tona asirin Kawunta Malamin coci

1
5580

Wata mawakiya mai suna DJ Switch ta wallafa wani rubutu a shafinta na Twitter, inda tayi bayanin yadda Kawunta, wanda yake fasto ne ya dinga lalata da ita tun tana ‘yar shekara 11 a duniya.

Ta ce Kawun nata mai suna Basil, a lokacin yana kamata ta karfin tsiya, inda kuma yake yi mata gargadi akan tayi shiru da bakinta kada ta bari wani yaji.

DJ Switch Photo Source: djswitch Instagram Page

Ta kara da cewa wannan shine karo na farko da ta fito ta bayyanawa duniya, ta ce mutane biyu ne kawai suka san da wannan labari na ta sune yayanta namiji da kuma ‘yar uwarta mace.

Ta ce:

“Na jima ban wallafa magana game da wannan ba, saboda ba abu ne mai dadi ba a gareni, amma dole na bayyana yanzu ga mutane yanzu ko na samu sawaba! A lokacin da mutane ke tambaya ‘wane irin kaya take sakawa? ‘Ina take zuwa? “mai yasa take ita daya?’ Ina matukar jin haushin irin wadannan mutanen.

Ban taba bayyana wannan labarin nawa ba in banda ‘yan uwana guda biyu da suka san da zancen, Emma da Lola. A lokacin da nake karama banfi shekara 11 ba a duniya lokacin, Kawuna ya dinga kamani yana kuma yi mini barazanar ba zai saka mini albarka ba idan har na sanar da wani abinda yake yi mini.

“Wannan shine abin mamakin, shi Malamin coci ne, sunan shi Basil. Na san tabbas dangina za suyi mamaki idan suka ga wannan. Duk wani mutum da yake a duniyar nan mace ce ta haife shi, kuma ina gaya muku duk macen da aka yiwa fyade ba da son ranta ba, to ta tsinewa duka dangin wanda yayi mata fyaden. Haka kuma akwai matan da suke yin haka, amma akasari an fi samun maza, saboda haka Allah ya tsinewa duk wasu mace da namiji da suke yiwa mutane fyade.

Post Source: djswitch Instagram Page

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here