Tun ina karama aka kulla maganar aurena da Adam A Zango – Cewar Jaruma Asiya Ahmad

0
498

Asiya Ahmad na daya daga cikin jaruman Kannywood mata da ke sharafi kafin masana’antar ta shiga halin walagigi, kuma kanwa ce ga fitacciyar jaruma Samira Ahmad, tsohuwar matar jarumi Ty Shaba.

Asiya ta taka rawa a fina-finai da dama wanda kuma kusan duka fina-finan da ta fito a ciki ta fito ne a matsayin tauraruwar da ke jan shirin, hakan kuwa ba karamin nasibi bane a harkar.

Kadan daga cikin fina-finan da ta fito sun hada da Me Kyau, Aure, Kanwa ta, Yankan Baya, Gida Uku da dai sauran su.

A wata hira da tayi da mujallar fim magazine, jarumar ta amsa tambaya game da dalilin da ya hana auren ta da Jarumi Adam A Zango, bayan kuma soyayyar su daddiya ce har kuma ta fito fili, inda ta bada amsa da cewa:

“To ni dai da ma a harkar fim ban taba yin soyayya da wani jarumi ba, kuma har yanzu haka nake. Shi kuma Adam A Zango, da man ya na zuwa gidan mu ne tun ina karama, ban ma yi wayo ba, kuma tun a lokacin yace yana sona zai aure ni. Aka tafi a haka har lokacin dana girma yana kan maganar.

“To ni dai daga baya abin da zan ce shine, Allah ne bai yi zan aure shi ba. Amma dai na san anyi maganar auren. Allah ne kawai bai yi za ayi auren ba.

An sake tambayar ta ko akwai wani dalili wanda take ganin shi ya hana ayi auren sai ta kara da cewa:

“Gaskiya dalilin da zan fada shine dai Allah bai sa za ayi ba. In ma akwai wani dalilin, kawai dai na san Allah ne yasa ba ayi ba.

A cikin hirar dai jarumar ta bayyana yadda ta taso da burin zama jaruma, amma ganin ‘yar uwarta na harkar yasa ta hakura daga baya kuma da ‘yar uwarta tayi aure sai ta tsundoma harkar da karfinta, kasancewar dama tuni tayi sabo da ‘yan fim din sanadiyyar ‘yar uwarta da mijin ‘yar uwartan duk jarumai ne ‘yan fim.

A karshe dai Asiya ta ja hankalin abokan sana’arta da su rika sanin mutuncin juna musamman abin da yafi ci mata tuwo a kwarya, yadda za aje a fadi magana akan ka, wacce kai baka san da ita ba, kuma sai ace kai kayi, inda ta ce hakan ya sha faruwa a kanta, sai dai wadanda suka santa idan sunji sai suce wannan ba halinta bane.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here