Tun da na auri danta ta saka mini karan tsana shi yasa na kasheta – Fatima

0
462

Wata matar aure mai shekaru 37 da aka cafke a ranar Litinin 27 ga watan Afrilun nan, bayan kama ta da laifin kashe surukarta mai suna Aishatu Umaru, a jihar Neja, ta bayyana dalilin da yasa tayi wannan aika-aika.

Fatima da mijinta Sani Umaru sun dan samu sabani a ranar 23 ga watan Afrilu, inda har ta kai ga aurensu ya rabu.

Fatima ta bayyanawa hukumar ‘yan sanda a lokacin da ake gabatar da bincike a kanta, cewar ta yanke shawarar kashe surukartan ne saboda tun da ta auri danta ta dauki karan tsana ta saka mata.

“Tunda na shigo gidan mijina ban san wani abu da ake kira da zaman lafiya ko kwanciyar hankali ba. Kowacce ranar Allah sai surukata ta samo wani tashin hankalin. Ban taba yin wani abu da ya burgeta ba, hakan ya saka na yanke shawarar kasheta kowa ma ya huta.

“Na san nayi abin da ko Allah ba zai yafe mini ba, amma duk abinda shari’a ta yanke a kaina yayi. Tunda bata barni na samu kwanciyar hankali a dakin mijina ba, ita ma Allah ba zai taba yi mata rahama ba.” Ta ce.

Yanzu haka dai tana hannun jami’an ‘yan sanda kuma za’a mika ta kotu nan ba dadewa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here