Tsoho dan shekara 80 ya yiwa marainiya ‘yar sheka 10 fyade a jihar Yobe

1
2020

Wani tsoho dan shekara 80 a duniya mai suna Mohammed Bara’u, daga kauyen Lawan Fannami dake yankin Gashu’a cikin jihar Yobe, ya shiga hannun ‘yan sanda bayan ya yiwa wata marainiya mai shekaru 10 fyade.

An ruwaito cewa mutumin wanda yake sana’ar sayar da itace, ya dinga kokarin yaudarar yarinyar da alewa amma bai samu nasara ba sai a wannan karon, inda ranar Lahadi bayan ya bukaci ta shiga dakinshi ta dauko masa wani abu sai ta amince.

Bayan shigar ta dakin sai ya bita ciki yayi lalata da ita da karfin tsiya.

An kama shi bayan wata kwamitin shari’ar Musulunci da kuma wasu kungiyoyin sa kai sun kai karar abinda yayi ga ‘yan sanda na karamar hukumar Bade.

An gabatar da gwaji a asibiti akan yarinyar wacce ta rasa iyayenta shekarun da suka gabata, sakamakon gwajin ya tabbatar da cewa tsohon ya yi mata fyaden.

Tsohon wanda ya amsa laifin shi na cewa ya yiwa yarinyar fyade sau daya, za a kai shi ofishin binciken manyan laifuka na CID dake garin Damaturu babban birnin jihar a yau Juma’a 19 ga watan Yuni.

Ana ta cigaba da samun kararraki na fyade dai a Najeriya duk kuwa da tashi tsaye da mutane suka yi na ganin cewa an dauki mataki akan masu wannan muguwar al’ada.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here