Tsofaffin masu gadi guda biyu sun yiwa yarinya ‘yar shekara 13 fyade a Kano

0
460

Jami’an hukumar Civil Defence na jihar Kano sun samu nasarar cafke wasu masu gadi guda biyu da aka kama da laifin yiwa wata yarinya ‘yar shekara 13 fyade a karamar hukumar Kumbotso dake jihar Kano.

Kwamandan rundunar NSCDC din, Abu Abdu, shine ya tabbatar da haka ga manema labarai, inda ya ce masu gadin akwai mai shekaru 56 da kuma mai shekaru 55.

A cewar Abu, masu laifin sun amsa laifinsu, inda suka ce dama can sun saba baiwa yarinyar kyautar naira dari biyu (N200) a duk lokacin da suke so suyi lalata da ita.

Abu yayi kira da rundunar ta shi da suyi kokarin wajen rage aika-aika ta cin zarafin mata da yara a jihar ta Kano.

Ya kara da cewa hukumar za ta cigaba da sanya ido a tashoshin motoci, kasuwanni da kuma wuraren da ba a kammala gini ba, inda ake tunanin za ayi yin irin wannan aika-aika.

A jiya ma mun kawo muku labarin wata yarinya mai suna Khadija da wani dan ahalinsu yayi mata fyade, inda hakan yayi sanadiyyar mutuwarta har lahira.

Yarinyar mai shekaru biyar ta gamu da ajalinta a lokacin da suke hanyar zuwa asibiti bayan mutumin yayi mata fyade, inda suka samu hatsari a hanyarsu ta asibitin.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here