Tsananin bakin ciki yasa magidanci ya kashe kansa bayan yaga iyalansa suna buda baki da ruwa a wannan wata na Ramadana

0
239
  • A yayin da kowa yake daukin wannan wata mai alfarma, sai ga wani bawan Allah shi kuma a cikin watan ne ya yanke hukuncin kashe kanshi
  • Mutumin ya kashe kanshi saboda tsananin bakin talauci da yake ciki shi da iyalansa
  • Matar mutumin ta bayyana cewa ya kashe kanshi saboda ganin yadda iyalansa suke bude baki da ruwa saboda rashin abinci

A kwanan nan shafin Twitter ya dauki dumi sosai akan labarin wani magidanci da tsananin bakin cikin talauci ya sanya ya kashe kanshi, bayan yaga iyalanshi suna yin buda baki da bakin ruwa.

Mutumin ya kashe kanshi saboda ya kasa samun kudin da zai basu abinci mai kyau a wannan lokaci.

Annobar Coronavirus dai ta sanya fargaba da tashin hankali ga talakawa da kuma kasashen da suke tasowa. Hakan ya samo asali ne saboda dokar hana fita da wasu kasashen suke sanyawa akan al’umma.

Rashin aikin yi shine babban abinda yafi sanya marasa karfi cikin tashin hankali.

Wannan annoba ta Coronavirus ta sanya mutane da yawa na kwanciya bacci da yunwa.

Aamna Bibi, matar marigayin, tayi hira da manema labarai a Samaa TV, inda ta bayyana yadda lamarin ya faru. Ta ce saboda babu abinci, ya sanya su da ‘ya’yansu dole suka dinga buda baki da bakin ruwa. Ta ce hatta abinci da sauran talakawa ke iya ci basu da kudin da za su iya siyowa.

Bayan mutumin ya gano halin da iyalan nashi suke ciki, yaga suna shan ruwa a lokacin Iftar, hakan ya sanya ya shiga damuwa. A cikin daren wannan rana yasha magani mai guba ya kashe kanshi.

Labarin wannan mutumi dai yana daya daga cikin labarai da suka fi tada hankalin jama’a a wannan lokaci da ake fama da Coronavirus.

Aamna Bibi ta kara da cewa a ranar da mijinta ya kash kanshi, sai da suka shafe kwanaki biyar ba tare da sun ci abinci ba.

Mutane sun nuna rashin jin dadinsu akan wannan abu da ya samu wannan bawan Allah.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here