Tsagwaron soyayyace tasa na auri matata ba wai kudi na bi ba – Malam Ali

0
3454

Jarumin fina-finan Hausa na Kannywood, Abdul’aziz Shu’aibu, wanda aka fi sani da Malam Ali na cikin shirin Kwana Casa’in da tashar Arewa24 take sanyawa, ya fito ya kare kanshi akan kace-ance da ake ta faman yi kan auren shi.

A kwanakin baya anyi ta kace-nace akan yadda aka yi ya amince ya auri matar da ta girme shi da shekara 12.

A wata hira da yayi da BBC Pidgin, jarumin mai shekaru 30 ya bayyana yadda ya hadu matarsa mai shekaru 42, sannan kuma ya bayyana yadda yayi watsi da bambancin shekaru domin ya kasance tare da ita.

“Idan na gaya muku cewa soyayyace tsakanina da Hajiya Bilkisu za ku yadda. idan ka samu wanda kake so, shekaru ba komai bane, to ni ban damu ba dan ta girme ni,” ya ce.

Ga me da yadda suka hadu kuwa, Abdulaziz ya bayyana cewa ita ce ta fara neman shi bayan ta ganshi a cikin wani shiri mai dogon zango da yayi suna a Arewa. Jarumin ya ce shi bai ga wani aibu ba akan abinda amaryar tasa tayi.

Jarumin wanda tuni dama yana da aure, ya ce Hajiya Bilkisu ita ce matarsa ta biyu, kamar yadda addinin Musulunci ya amince namiji ya auri mace fiye da daya.

Abdulaziz ya kuma shawarci maza da su fito su sanar da mata gaskiya musamman ma idan mutum yana soyayya da wacce ta girme shi, ba wai mutum ya dinga kallonsu a matsayin wadanda zai dinga samun kudi a wajensu ba.

“Yawancin samarin mu suna kallon matan da suka girme su a matsayin Sugar Mummies, kuma hakan ba daidai bane, kowa yana iya samun soyayya a ko ina,’ ya ce.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here