Tozarci ne saka bidiyon tsiraici na yaran da aka yiwa fyade – Rukayya Dawayya

1
584

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa da tauraruwarta ta haska a shekarun baya, wato Rukayya Dawayya, ta nuna bacin ranta akan yadda ake cin zarafin yara a wannan lokacin a shafukan sada zumunta.

Jarumar ta bayyana hakane a wani sabon bidiyo, inda ta ce ba ta san mai yake damun al’ummarmu ba da za’a dauki bidiyon yara mata kanana da aka yiwa fyade a dinga sanyawa a shafukan sadarwa.

Dawayya ta ce wannan ba karamin cin zarafi bane da tozarci, ta ce ba wai yara kanana kawai ba, hatta tsofaffi wadanda suka yiwa yaran fyade taga an sanya bidiyonsu tsirara haihuwar uwarsu a shafukan sadarwa.

Jarumar dai ta nuna cewa da yawa daga cikin mutanen da suke yiwa wasu fyade wasu basu san da cewa sunyi bama, inda ta alakanta hakan da cewa wasu hau ne yake hawa kansu.

Dawayya ta ce duka irin wannan abu na rashin tunani yana faruwa a yankin Arewa ne, inda tace baza ka taba ganin mutanen Kudu sun dauki mutanensu tsirara sun sanya a shafukan sadarwa ba.

Ta ce wannan abu ba daidai bane kwata-kwata, kuma ya kamata mahukunta a Najeriya su fito su dauki mataki akan wannan abu.

Ta ce hakkine a kanta a matsayinta na Musulma ‘yar Arewa ta fito ta fadi gaskiya, inda tace duk wanda ma bai sani ba yaje yayi bincike akan abinda Allah ya ce kan irin wannan cin zarafi.

Ta ce kowa da irin tashi jarabtar da kuma kaddarar da Allah ya dora mishi a duniya, inda ta ce babu wanda yasan wace irin jarrabawa Allah zai yiwa mutane a nan gaba.

Ta ce muji da masifun da suke damun mu mana a Arewa, ta ce bamu kashe wannan wutar ba muna ta kara ruruta wata wutar bala’in a kanmu.

To Allah dai ya kyauta, ya kuma kawo karshen wannan matsala a kasar mu baki daya.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here