To fah: ‘Yan sanda sun kama wanda ya jagoranci zanga-zanga a Katsina

0
351

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama Nastura Ashir Sharif, mutumin da ya jagoranci zanga-zangar lumana a jihar Katsina jiya Talata.

A wata sanarwa da kungiyar CNG ta fitar kungiyar hadin guiwar kungiyoyin arewa ta wallafa shafinta na Facebook, ta bayyana cewa an kama shugaban nasu an wuce da shi zuwa Abuja jim kadan bayan kammala zanga-zangar lumanar a Katsina.

“Nastura Ashir Sharif, shugaban masu kungiyar hadin guiwar kungiyoyin, yanzu haka yana tsare a helkwatar ‘yan sanda dake Abuja.

“Ya nuna rashin goyon bayanshi akan kashe-kashen da ake yine kawai,” cewar sanarwar ta su.

Daya daga cikin ‘yan kungiyar, wanda yayi magana da wakilin Daily Trust, ya ce kwamishin ‘yan sandan jihar ne ya dauke shi daga Abuja zuwa Katsina.

“Kwamishinan ‘yan sanda ya sanar da shi cewa shugaban hukumar ‘yan sanda yana so ya gana da shi a Abuja, inda suka tafi tare.

“Bayan sun isa Abuja sun tsare shi a helkwatarsu,” ya ce.

A wata hira da aka yi da kungiyar, ta ce zanga-zanga ita ce kawai abinda gwamnati take ganewa game da wannan kashe-kashen da ake yi a arewa.

A jiya Talata dai dubunnan mutane suka gabatar da zanga-zangar lumana a jihar ta katsina, inda suka dinga kira ga shugaba Buhari da Masari da su sauka daga kujerunsu.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here